Crypto ta sa Zhao ya zama mutum na 15 a masu kudin Duniya, ya ribanya Dangote sau 4

Crypto ta sa Zhao ya zama mutum na 15 a masu kudin Duniya, ya ribanya Dangote sau 4

  • Rahotanni sun nuna cewa Changpeng Zhao shi ne na 15 a sahun manyan masu kudin Duniya a 2022
  • Shugaban kamfanin Binance ya mallaki kusan Dala biliyan 100 a sakamakon gawurtar da Crypto ta yi
  • Arzikin Zhao kusan ya nunka na Aliko Dangote hudu a halin yanzu, Dangote ya mallaki kusan $20bn

Shugaban kamfanin Binance, Changpeng Zhao mai shekara 44 da haihuwa, ya shiga sahun gawurtattun masu kudin da ake ji da su a fadin Duniya.

Wani rahoto da Intel Region ta fitar a makon nan ya nuna Changpeng Zhao ya na cikin manyan attajirai 15 na Duniya, mallaki sama da Dala biliyan 96.

Jaridar tace dukiyar shugaban kamfanin na Binance a wancan lokaci bai wuce Dala miliyan 15 ba.

Shekaru shida da suka wuce, Aliko Dangote shi ne mai kudin Afrika (har gobe), a wancan lokaci Changpeng Zhao ma’aikaci ne da yake karbar albashi.

Kara karanta wannan

Zaben APC: Ka da ku raina mana hankali fa – Kungiyar PGF ta fadawa su Mala Buni

Rahoton da Bloomberg ta fitar a karshe ya nuna cewa babban mai kudin Afrika, Aliko Dangote ya na da kusan $20bn, 20% na abin da Zhao yake da shi a yau.

Yanzu maganar da ake yi, Zhao ya sha gaban Mukesh Ambani a jerin masu kudin Duniya, ya kama hanyar kamo kafar Mark Zuckerberg da Larry Page.

Changpeng Zhao
Changpeng Zhao da Aliko Dangote Hoto: www.coindesk.com, www.one.org
Asali: UGC

Binance ya gawurta

Masu amfani da kudin yanar gizo na Cryptocurrency da Changpeng Zhao ya kirkiro, su kan kira shi CZ. Dukiyar kamfaninsa sai da ya karu da 1250% a 2021.

A shekarar 2021 kawai, ana hasashen Binance ya samu kudin shiga na Dala biliyan 20. A kwana guda, sai da kamfanin na Crypto ya yi cinikin fam $170bn.

Sai dai gwamnatocin kasashen Birtaniya, Jafan da Jamus sun sa ido a kan aikin kamfanin. An haramta aikinsu a Sin, yayin da ake bincikensu a Amurka.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Yan bindiga sun kai hari Plateau Poly, sun kwashe dalibai

Changpeng Zhao ya ki cewa uffan

Bloomberg tace Zhao ya ki cewa komai a game da rahotannin da ake ji a kan adadin dukiyarsa da na kamfaninsa, yana zargin a kan zuzuta yawan kudinsa.

Binance ya fitar da jawabi ya ce yanzu aka fara aiki da Crypto, don haka alkaluma suke tangal-tangal, babu tabbacin abin da yake yau, ya zama shi ne gobe.

Mai BUA ya yi gaba

Kwanaki kun ji cewa masu hasashe su na ganin cewa Alhaji Abdul Samad Rabiu ya zama na biyu yanzu a rukunin masu kudin kasar nan, ya zama na biyu.

Abdul Samad Rabiu ya mallaki sama da Dala biliyan 7, kusan Naira tiriliyan 3 ya ba baya kenan Read more:

Asali: Legit.ng

Online view pixel