Kasashen Duniya za su bada gudumuwa wajen kawo zaman lafiya a Zamfara inji Matawalle

Kasashen Duniya za su bada gudumuwa wajen kawo zaman lafiya a Zamfara inji Matawalle

  • Kasashen Duniya za su taka rawar gani domin a samu kwanciyar hankali da aminci a yankin Zamfara.
  • Gwamnatin Zamfara ta bada wannan sanarwa bayan Gwamna Bello Matawalle ya hadu da Tony Blair.
  • Tony Blair zai dage wajen ganin sauran kasashe sun ba mutanen Zamfara gudumuwa da goyon baya.

UK - Tsohon Firayim Ministan Birtaniya, Tony Blair, ya yi alkawarin tattaro kasashen Duniya domin su taimakawa Zamfara a kan halin da jihar ta shiga.

Jaridar Tribune ta rahoto cewa Tony Blair ya sha alwashin ganin Duniya ta taimakawa Zamfara da goyon baya da dukiya wajen shawo matsalar rashin tsaro.

Tsohon shugaba Blair zai kuma dage wajen ganin an kawowa mutanen Zamfara agaji na musamman.

Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana hakan ne a wani jawabi da ya fito daga bakin mai magana da yawun bakin mai girma gwamna, Malam Zailani Bappa.

Bappa ya fitar da jawabi a ranar Asabar, 6 ga watan Nuwamba, 2021, bayan ganawar da Bello Muhammadu Matawalle yayi da Tony Blair a kasar Ingila.

Matawalle
Tony Blair da Bello Matawalle Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Zailani Bappa ya fitar da jawabi

“Cibiyar Blair Institute for Global Change ta yabawa gwamna Bello Matawalle a kan salon da ya dauka na shawo kan rikicin da ke jihar.”
“Blair, wanda ya karbi bakuncin gwamna a cibiyar da ke Landan, yace gwamnan ya burge shi da yake neman taimakon kasashen Duniya.”
“Ya yi alkawari zai yi amfani da damarsa wajen samun goyon-baya, gudumuwa da jawo masu zuba hannun jari zuwa Zamfara.” – Zailani Bappa.

Daily Nigerian tace Bappa yace wannan zai zama gudumuwar da cibiyar ta bada wajen samun zaman lafiya da kawo cigaba a jihar da take fama da kalubale.

Matawalle ya yaba da irin kokarin Blair Institute for Global Change na taimakawa kasashen Afrika irinsu Ghana, Togo, Habasha, da kasar Cote d’Ivoire.

'Yan bindiga sun zama 'yan ta'adda

Kwanakin baya aka ji labari cewa 'yan majalisar tarayya sun ba Gwamnatin Muhammadu Buhari wa’adi, ta dauki mataki a kan masu sata da kashe mutane.

Hon. Abdulrazaq Namdas yace ta’adin ‘Yan bindiga yana neman zarce abin da ‘Yan Boko Haram suka yi, yace ya kamata a sa su a cikin jerin 'yan ta'adda.

Asali: Legit.ng

Online view pixel