Aisha Musa
9391 articles published since 09 Agu 2016
9391 articles published since 09 Agu 2016
Majalisar Dattawa ta bayyana cewa tana iya bayar da sammaci ga Shugabannin Hukumar Tashar Jiragen Ruwa ta Najeriya (NPA) da NIMASA kan batan kudade a kulawarsu.
Gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu, ya ce 'yan kudu ba za su goyi bayan duk wata jam'iyyar siyasa da ta zabi dan takarar shugaban kasa na arewa a zaben 2023 ba.
Hukumar Korafi da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano, PCACC, ta ce ta kama manyan motoci biyu na masara da ake zargi sun gurbata a kasuwar Dawanau.
Manjo CL Datong, wanda aka yi garkuwa da shi lokacin da 'yan bindiga suka kutsa cikin Kwalejin sojoji na Najeriya (NDA) da ke Kaduna, ya sake samun 'yanci.
A matsayin jam’iyya da ke ba da lada ga masu yi mata biyayya, APC mai mulki na iya ba Femi Fani-Kayode damar tsayawa takarar shugaban kasa ko mataimakinsa.
Biyo bayan hauhawar bashin da ake samu a kasar nan, Sanata Ndume ya mayar da martani ga lamunin ciyo bashin gwamnatin tarayya na waje a lokutan baya -bayan nan.
Mahara sun kashe Abubakar Abdullahi, shugaban kungiyar Miyetti Allah a karamar hukumar Lere ta jihar Kaduna bayan sun yi garkuwa da shi tare da neman N20m.
Akalla gwamnonin jihohi tara daga yankin kudancin kasar sun fito fili sun nuna adawa da karbar Harajin kaya (VAT) da Hukumar Kula da Haraji ta Tarayya ke yi.
Shugaban watsa labarai kuma daraktar harkokin jama’a na NCF, Dr. Yunusa Tanko, a ranar Alhamis, 16 ga Satumba, ya tabbatar da cewa za a bayyana sabuwar tafiya.
Aisha Musa
Samu kari