'Yan sanda sun cafke wani sojan bogi dan shekara 28 dauke da bindiga da sauransu

'Yan sanda sun cafke wani sojan bogi dan shekara 28 dauke da bindiga da sauransu

  • Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta cafke wani sojan bogi da ke nuna kansa a matsayin jami’in rundunar sojin Najeriya
  • An gano kayan sojoji daban-daban ciki har da bindiga AK-49 da mujalla biyu a hannun wanda ake zargin
  • An damke sojan gonan wanda ya fito daga jihar Filato tare da kakin sojoji a karamar hukumar Lafia ta jihar Nasarawa

Lafia, Nasarawa - 'Yan sanda a jihar Nasarawa sun cafke wani sojan bogi, Timothy Emmanuel wanda ke yawo cikin kayan sojoji.

Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito cewa matashin mai shekaru 28 ya kasance yana yiwa wani jami'in sojan Najeriya sojan gona, a cewar kwamishinan 'yan sandan jihar, Adesina Soyemi.

'Yan sanda sun cafke wani sojan bogi dan shekara 28 dauke da bindiga da sauransu
'Yan sanda sun cafke wani sojan bogi dan shekara 28 dauke da bindiga da sauransu Hoto: @channelsforum
Asali: Facebook

Soyemi ya ce an gurfanar da Emmanuel, wanda dan asalin jihar Filato ne a ranar Juma’a, 17 ga watan Satumba, tare da wasu mutane 60 da ake zargi da aikata laifuka daban -daban.

Kara karanta wannan

2023: Fitaccen dan majalisar arewa ya bayyana dalilin da ya sa APC ke zawarcin Jonathan, ya yi magana akan kudirin Tinubu

An samu bindiga kirar AK-49, mujalla biyu da motar Toyota Corolla yayin da mai laifin mai shekaru 28 ke tafiya akan hanyar B.A.D a karamar hukumar Lafiya, jaridar The Nation ta ruwaito.

Soyemi ya bayyana cewa wanda ake zargin yana aikata miyagun ayyuka a Karu da Lafiya kafin a kama shi.

A cewarsa, ana binciken Emmanuel a sashin binciken manyan laifuka na jihar da ke Lafiya.

Rundunar soji ta kai farmaki sansanin ‘yan bindiga, ta ceto babban sojan da aka sace a NDA

A wani labarin, mun ji cewa Manjo CL Datong, wanda aka yi garkuwa da shi lokacin da 'yan bindiga suka kutsa cikin Kwalejin horar da sojoji na Najeriya (NDA) a Kaduna, a watan da ya gabata, ya samu ‘yanci, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Rundunar soji ta kai farmaki sansanin ‘yan bindiga, ta ceto babban sojan da aka sace a NDA

An kashe manyan jami’an biyu a lamarin wanda ya faru a ranar 24 ga Agusta, 2021.

A daren Juma'a, 17 ga watan Satumba, Mataimakin Daraktan Hulda da Jama'a na Runduna ta 1, Sojojin Najeriya, Kanal Ezindu Idimah, ya ce sojoji sun ceto Datong, jaridar Punch ta ruwaito.

Ya ce ayyukan da suka kai ga kubutar da shi sun kai ga rusa sansanonin ‘yan ta’adda da aka gano a yankunan Afaka- Birnin Gwari na jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng