Gagarumin matsala ya fara yayin da majalisa ta yi barazanar kama wasu manyan nade-naden Buhari
- Babbar majalisar dokokin Najeriya, Majalisar Dattawa, ta ce za a iya kama shugabannin NPA da NIMASA idan ba a yi hankali ba
- Kwamitin majalisar dattawa kan asusun gwamnati ya bayyana hakan a ranar Juma'a, 17 ga watan Satumba, lokacin da shugabanta, Matthew Urhoghide, ya zanta da manema labarai
- Urhoghide ya bayyana cewa Shugaban NPA da DG na NIMASA duk sun ki su bayyana a gaban majalisar don bayanin kudaden da ake zarginsu a kai na N10 biliyan
Abuja - Ana iya kama manyan jami'an hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta Najeriya (NPA) da Hukumar Kula da Tsaron Jiragen Ruwa ta Najeriya (NIMASA) nan ba da jimawa ba.
Sanata Matthew Urhoghide, shugaban kwamitin majalisar dattawa akan asusun gwamnati, ya bayyana yiwuwar haka a ranar Juma'a, 17 ga watan Satumba a Abuja, jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Urhoghide ya yi bayanin cewa hakan ya zama dole bayan da shugabanin hukumomin suka ki su bayyana a gaban kwamitinsa don amsa tambayoyi kan naira biliyan 10 da miliyan 814 a karkashin kulawarsu.
Ya bayyana cewa shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen sanya hannu kan sammacin kama su idan bukatar hakan ta taso, jaridar The Nation ta ruwaito.
Kalamansa:
"Ga rahoton 2016, 2017 da 2018 na AuGF da muke la'akari da shi a yanzu, za mu tabbatar hukumomin da suka yi kuskure wadanda suka hada da NPA, NIMASA, da sauransu sun bayyana.
"Yana iya kasancewa kan kunyata jami'an lissafin kudade na wadannan hukumomin. A shirye muke mu bayar da sammacin kama su saboda na san shugaban majalisar dattijai yana da kyakkyawar niyyar sanya hannu kan sammacin kamu, musamman kan hukumomin da aka samu da irin wannan laifin yayin da muke nazarin rahoton 2015.”
PDP ta samu abin yin magana, Ministan Buhari yace ana sata salin-alin a Gwamnatin APC
A wani labarin, jam’iyyar adawa ta PDP tace bayanan da aka ji Ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya na yi a kan gwamnatin APC, sun tabbatar da abin da ta ke fada.
PDP ta bakin Mai magana da yawunta, Kola Ologbondiyan ta ce abin da Ministan tarayyar ya fada, ya gaskata ikirarinta na cewa ana sata a gwamnatin nan.
A ranar Litinin, 30 ga watan Agusta, 2021, jaridar The Cable ta rahoto sakataren yada labaran na APC, Kola Ologbondiyan, ya na maida wa Ministan martani.
Asali: Legit.ng