Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari zai tafi New York don halartar taron UNGA a ranar Lahadi

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari zai tafi New York don halartar taron UNGA a ranar Lahadi

  • Jirgin Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai tashi daga Abuja zuwa birnin New York, a ranar Lahadi, 19 ga watan Satumba
  • Buhari zai halarci taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya karo na 76
  • Adesina ya bayyana cewa shugaban kasar zai kuma gudanar da tarurruka tare da wasu shugabannin tawagogi

Aso -Rock, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bar Abuja a ranar Lahadi, 19 ga watan Satumba zuwa birnin New York a Amurka.

Legit.ng ta rahoto cewa shugaban kasar zai halarci taro na 76 na babban zauren Majalisar Dinkin Duniya (UNGA76). An bude taron ne a ranar Talata, 14 ga watan Satumba.

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari zai tafi New York don halartar taron UNGA a ranar Lahadi
Shugaba Buhari zai tafi New York don halartar taron UNGA a ranar Lahadi Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Taken taron UNGA na wannan shekarar shine, “Building Resilience Through Hope – To Recover from COVID-19, Rebuild Sustainably, Respond to the Needs of the Planet, Respect the Rights of People and Revitalize the United Nations.”

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Me niyyar takarar kujerar shugaban kasa a 2023 ya mutu

Femi Adesina, mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, a cikin wata sanarwa a ranar Asabar, 18 ga Satumba, ya ce shugaban kasar zai yi jawabi ga Majalisar yayin muhawara a ranar Juma’a, 24 ga Satumba inda zai yi magana kan taken taron da sauran batutuwan duniya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

“A yayin taron, shugaban na Najeriya da mambobin tawagarsa za su halarci wasu muhimman tarurruka kamar; Taron murnar shekara 20 da kafa dokokin haramta wariyar launin fata.
“Tawagar za kuma ta halarci Babban taron tsarin abinci; Tattaunawa kan Makamashi; da babban taro don tunawa da haɓaka ranar duniya don cire Makaman Nukiliya.
“Shugaban kasar zai kuma yi tarurruka da wasu shugabannin tawaga da na kungiyoyin ci gaban kasa da kasa.
“Zai samu rakiyar Ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyeama; Babban Lauyan Kasa kuma Ministan Shari’a Abubakar Malami (SAN); da Karamin Ministan Muhalli, Sharon Ikeazor zuwa New York.

Kara karanta wannan

Gagarumin matsala ya fara yayin da majalisa ta yi barazanar kama wasu manyan nade-naden Buhari

“Hakanan a cikin tawagar Shugaban kasar akwai: Mai ba da shawara kan harkokin tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno (mai ritaya); Darakta Janar na Hukumar Leken Asiri ta Kasa, Amb. Ahmed Rufai Abubakar; Shugabar Hukumar Kula da 'Yan Najeriya mazauna kasashen waje, Abike Dabiri-Erewa da Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban kasa kan SDGs, Misis Adejoke Orelope-Adefulire.
"Ana sa ran Shugaba Buhari zai dawo kasar a ranar Lahadi, 26 ga watan Satumba."

A wani labari na daban, Barista Olusegun Bamgbose, me niyyar takarar kujerar shugaban kasa na sabuwar jam'iyyar Peoples Democratic Party (NNPP) ya rasu.

Bamgbose wanda ya kasance jagoran kungiyar masu fafutukar neman shugabanci nagari (CAGG) ya rasu a ranar Juma'a, 17 ga watan Satumba, bayan gajeriyar rashin lafiya, Daily Post da PM News sun ruwaito.

Da take magana kan rasuwar dan siyasar, Gidauniyar FENRAD, ta bayyana shi a matsayin babban muryar lamuran shugabanci nagari da fafutukar kare haƙƙin ɗan adam.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: ‘Yan bindiga sun kai hari garin Kaduna, sun kashe shugaban Miyetti Allah

Asali: Legit.ng

Online view pixel