Fitaccen Sanatan APC ya nuna damuwa kan yadda majalisa ke saurin amincewa Buhari ya ciyo bashi

Fitaccen Sanatan APC ya nuna damuwa kan yadda majalisa ke saurin amincewa Buhari ya ciyo bashi

  • Sanata Ali Ndume ya nuna damuwarsa kan yadda gwamnatin tarayya ke karbo bashi a cikin matsanancin halin tattalin arzikin da ke fuskantar kasar
  • Ndume bai ji dadin yadda majalisar kasa ta gaggauta mayar da martani kan rokon da shugaba Buhari ya yi na karbo basussuka ba
  • A halin da ake ciki, martabar bashin Najeriya na ci gaba da karuwa yayin da shugaban kasa ya gabatar da wani sabon bukatar ranto kudi a gaban majalisar dattijai

FCT, Abuja - Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Sojoji, Sanata Ali Ndume, ya ce ya damu da yadda majalisar dokokin Najeriya ke tafiyar da batun ciyo basussuka da rance da gwamnatin tarayya ke yi.

Channels TV ta ruwaito cewa Ndume yayi wannan furuci ne a ranar Alhamis, 16 ga watan Satumba, inda ya nuna matukar damuwa game da yadda majalisar kasa ta dauki bukatar ciyo bashin na shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Fitaccen Sanatan APC ya nuna damuwa kan yadda majalisa ke saurin amincewa Buhari ya ciwo bashi
Fitaccen Sanatan APC ya nuna damuwa kan yadda majalisa ke saurin amincewa Buhari ya ciwo bashi Hoto: Senator Mohammed Ali Ndume Support Forum
Asali: Facebook

A watan Yuli ne Majalisar Dattawa ta amince da shirin karbo bashin gwamnatin tarayya na shekarar 2018-2020 na dala biliyan 8.3 da Yuro miliyan 490.

Jaridar Premium Times ta kuma ruwaito cewa Ndume abun da ya kuma fi damun shi shine cewa babu abin nunawa wanda za a ce an yi da kudin da aka ranto.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kuma ce ya kamata a zauna sosai ayi nazari sannan a nemi sanin ra'ayin mutanen da ake wakilta ba wai kawai majalisa ta zauna tace ta amince da ciyo bashin ba.

Ndume ya ce:

“Ciyo bashi ba laifi bane amma lokacin da adadin bashin ya ƙaru wanda na fahimci yana kusa da kashi 80 zuwa 90 cikin ɗari, dole ne mutum ya yi taka tsantsan.
“Abin da ke damuna kuma shine yadda Majalisar Dattawa ke bi da lamarin. Majalisar dattijai a ma'anarsa gidan ne na shawara a lokacin da abubuwa irin wannan suka zo, ba kawai mu hanzarta mu ce saboda ana yi maka kallon mutum nagari sai kayi hanzarin amincewa da shi ba"

Tattalin Arzikin Najeriya Ba Zai Samu Cigaba Ba Idan Ba Mu Ciyo Bashi Ba, Gwamnatin Tarayya

A gefe guda, mun ji a baya cewa ministan kudi, kasafi da tsare-tsaren kasa, Zainab Ahmed, tace cigaban tattalin arziki na kashi 5.01% da aka samu a rukunin shekara na biyu, 2021 zai samu koma baya idan ba'a ciyo bashi ba.

Ministan tace bashin da gwamnati ke ciyo wa tana zuba shi ne a ɓangaren gina muhimmman ayyukan kasa dake samar da aikin yi, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Da take jawabi a Abuja ranar Litinin, a wani taron manema labarai tare da ministan yaɗa labaru, Ali Muhammed, da wasu kusoshin gwamnati, Zainab tace:

"Gwamnatin tarayya tana farin cikin yadda tattalin arziki da harkokin kasuwanci suka fara komawa kamar da tun bayan ɓarkewar korona."

Asali: Legit.ng

Online view pixel