Gwamnati ta kama tare da kwace hatsi mai guba a jihar Kano

Gwamnati ta kama tare da kwace hatsi mai guba a jihar Kano

  • Gwamnatin jihar Kano ta yi ram da gurbatattun hatsi a babbar kasuwar hatsi ta Dawanau
  • Mukaddashin shugaban hukumar korafe-korafe da cin hanci da rashawa ta jihar Kano (PCACC), Barista Mahmoud Balarabe, ya ce an kama wasu mutane kan haka
  • Ya bayyana cewa an gano shagon ne bayan sun samu bayanan sirri kan yadda ake safarar gurbatattun hatsi a tirela biyu zuwa kasuwa

An gano ma'ajiyar gurbatattun hatsi a babbar kasuwar hatsi ta Dawanau, Kano, sannan an kama wasu da ake zargi da hannu a lamarin.

Mukaddashin shugaban hukumar korafe-korafe da cin hanci da rashawa ta jihar Kano (PCACC), Barista Mahmoud Balarabe, ya ce jami’an sun gano shagon ne bayan sun samu bayanan sirri kan yadda ake safarar gurbatattun hatsi a tirela biyu zuwa kasuwa a yammacin Alhamis.

Kara karanta wannan

'Yan sanda za su gurfanar da wata matashiya ‘yar shekara 25 da ke yi wa ‘yan bindiga leken asiri a Katsina

Gwamnati ta kama tare da kwace hatsi mai guba a jihar Kano
Gwamnati ta kama tare da kwace hatsi mai guba a jihar Kano Hoto: Kano state government
Asali: UGC

Ya ce an kama direban da abokin mai kayan, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Da yake jagorantar 'yan jarida a ranar Juma'a zuwa zagayen shagon, ya ce an sami buhunan gurbatattun masara da gero.

Ya ce:

“Masarar tana da duhu sosai kuma tana bayyana guba sosai. Abin da suke yi anan shine su haɗa mai guba da ɗan kaɗan daga cikin masu kyau sannan su dinke jakar kafin su kai shi wani kamfani inda suke niƙa shi don amfani. Duk tsawon wannan lokacin, mutane suna cin wannan guba.”

Ya ce a wani bangare na ci gaba da binciken hukumar, za a gayyaci shugabancin kasuwar “musamman masu kula da masara da gero; za mu zauna da su mu san abin da suka sani game da wannan batu. ”

Kara karanta wannan

'Yan Majalisa na Kudu sun yi taro a gidan Ekweremadu kan ceto Nnamdi Kanu

Ya kuma ce ana ci gaba da kokarin cafke mai wannan kayan da shagon, wanda aka bayyana sunansa da Adamu Maigari.

Shugaban ya bukaci mutanen jihar da su bayar da sahihan bayanai ga Hukumar da sauran hukumomin tsaro kan kayayyaki marasa inganci don kare lafiyar jama'a, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kudi kimanin N350m sun yi batan dabo daga baitul malin kotun Shari'a a Kano

A wani labari na daban, kudi Sama da N345million sun yi batan dabo daga asusun babbar kotun Shari'a a jihar Kano, a cewar rahoton gidan rediyon Freedom.

Babban Alkalin kotun Shari'ar jihar Grand Khadi Tijjani Yakasa ya tabbatar da hakan inda yace an kai karan lamarin ofishin sauraron kararraki da yaki da rashawa na Kano domin bincike.

Sakataran kotun, Haruna Khalil, ya bayyana cewa tuni an kafa kwamitin bincike domin gudanar da bincike kan lamarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel