Shugabancin 2023: Manyan mukamai da Fani-Kayode zai iya samu a matsayin tukwicin sauya sheka zuwa APC
- Bayan sauya shekarsa zuwa APC daga PDP, masana harkar siyasa sun fara hasashe kan tukwicin da jam'iyyar mai mulki za ta iya baiwa Femi Fani-Kayode
- Ana ganin APC za ta baiwa Fani-Kayode damar zama dan takarar shugaban kasarta ko kuma mataimakin shugaban kasa a babban zaben kasar mai zuwa
- An dai san jam'iyya mai mulki da ba da lada ga waɗanda suka yi mubaya’a da nuna biyayya gare ta
Duk da cewa bai nuna aniyar shiga takarar shugaban kasa na 2023 ba, Femi Fani-Kayode ta hanyar sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na iya yin burin samun wani babban matsayi a mulkin kasar.
Abu na farko, da ya zama dole a fadi shine cewa an san jam’iyya mai mulki da bayar da tukwici ga waɗanda suka yi mubaya’a da nuna biyayya ga dandalin ta.
A halin da ake ciki, tsohon ministan sufurin jiragen sama na iya samun lada da tikitin takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC gabanin babban zabe mai zuwa ko kuma a ƙalla a ba shi damar zama abokin takarar duk wanda aka zaɓa ya zama dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar.
Shugaban kasa
Tare da kiraye -kirayen da ake yi na neman a karkatar da kujerar shugaban kasa zuwa yankin kudancin kasar, APC na iya mika FFK a matsayin amsa ga wannan kira.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Aƙalla, ta wannan hanyar, jam’iyya mai mulki ba za ta rasa komai ba, tunda za ta gamsar da sha’awarta na ci gaba da kasancewa a tsakiya yayin da take adalci ga bukatar juya madafun iko.
Mataimakin Shugaban kasa
Idan APC na jin cewa kujerar shugaban kasa ta yi girma da za ta ba sabon shiga, za ta iya mara masa baya don yin takara tare da zababben dan takarar kujerar.
Da alama wannan zai yi ma'ana sosai idan mutum yayi la'akari da cewa a 'yan kwanakin nan Fani-Kayode yana ta kulla alaƙa mai ƙarfi da Gwamna Yayaha Bello wanda ke hararar kujerar Shugaba Buhari.
Don haka, tsohon ministan ba zai samu cikas ba wajen yiwa kasarsa ta gado hidima a matsayin mataimakin shugaban ƙasa tare da abokinsa na Kogi.
Abinda yasa na bar PDP, gwamnonin PDP 3 da na sha alwashin ja zuwa APC, Fani Kayode
A wani labarin, tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, ya sha alwashin tarkata gwamnonin jihohin Oyo, Bauchi da na Enugu zuwa jam'iyya mai mulki bayan komawarsa a yau.
Gwamnan jihar Yobe, kuma shugaban kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar APC, Mai Mala Buni ne ya gabatar da tsohon ministan ga shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara.
Fani-Kayode wanda ya zanta da manema labarai, ya ce lokaci yayi da ya dace ya hada kai da shugaban kasa wurin ciyar da Najeriya gaba, Daily Nigerian ta ruwaito.
Asali: Legit.ng