Aisha Musa
9376 articles published since 09 Agu 2016
9376 articles published since 09 Agu 2016
Sufeto Janar na ‘an sandan Najeriya, Usman Baba, ya yi karin haske kan jinkirin da aka samu na aiwatar da karin albashi ga jami’an rundunar ‘yan sandan kasar.
Fitacciyar ‘yar wasan fina-finan Hausa ta kannywood, Fatima Isa da akafi sani da Teema Yola, za ta shiga daga ciki. Jaruma Umma Shehu ce ta sanar da labarin.
Kotun majistare ta soke belin da ta baiwa tsohon Kwamishinan Ayyuka na Jihar Kano, Injiniya Mu’azu Magaji wato Dan Sarauniya saboda kin zuwa zama har sau uku.
Na kusa da shugaba Buhari, Sanata Abu Ibrahim ya ce Gwamna Fayemi da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ba za su iya tsayawa takara da Bola Tinubu ba.
Akwai alamu da ke nuna cewa jam’iyyar PDP na kokarin lallaba manyan tsoffin mambobinta da suka sauya sheka zuwa wasu jam’iyyun siyasa domin su dawo cikinta.
Tsohon shugaban majalisar dattawa, Dakta Abubakar Bukola Saraki, ya ce zai bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa kafin karshen wannan wata ta Maris.
APC na shirin maka tsoffin mambobinta kamar irin su Saraki, Tambuwal, Ortom da Obaseki a gaban kotu kan sauya sheka zuwa PDP, tana so a haramta masu takara.
Wata kungiyar kudu maso gabas ta bayyana cewa akwai yiyuwar yankin ya fice daga kasar, idan dan kabilar Igbo bai gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari ba a 2023.
Tsohon dan majalisar wakilai daga Kaduna, Samaila Suleiman, ya sauya sheka daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki. Bai fadi ina zai koma ba.
Aisha Musa
Samu kari