Ahmad Yusuf
10109 articles published since 01 Mar 2021
10109 articles published since 01 Mar 2021
Wata tankar dakon mai da ta fashe fetur ya fara kwarara ta kama da wuta bayan mutane sun gana kewaye ta, ana fargabar rasa gomman rayuka a jihar Neja.
Rahotanni sun nuna cewa an fara samun saukin tsadar kayan abinci a babban kaauwar Kaduna kwanaki kasa da 20 bayan shigowar sabuwar shekara watau 2025.
Wasu ƴan damfarar yanar gizo da aka fi sani da Yahoo Boys sun far wa dakarun hukumar EFCC ba zato ba tsammani, sun kashe jami'i ɗaya wani na kwance a asibiti.
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta sasanta rikici masu tarin yawada suka haɗa da rigimgimun aure, rabon gado da rikici tsakanin al'umma a 2024, ta shirya aiki a 2025.
Rundunar ƴan sanda ta damke wasu matasa su biyar bisa zarginsu da bugun wani matashi har lahira a wurin shagalin bikin aure, za a maka su a kotu bayan bincike.
Sakamakon hauhawar farashin gangar ɗanyen mai a kasuwar duniya, farashin tataccen ɗanyen man fetur ya tashi a wuraren ƴan kasuwa bayan ƙarin da Ɗangote ya yi.
Yan majalisa sun nuna ɓacin ransu kan rashin kai masu takardun kasafin kuɗin ma'aikatar albarkatun man fetur, minista ya ba da hakuri ranar Alhamis.
Wasu mahara da ake zargin masu garkuwa ne sun sace matar mataimakin sufetan ƴan sanda na ƙasa mai ritaya a gidanta da ke jihar Ogun a ranar Juma'a.
Jam'iyyar LP ta musanta raɗe-raɗin da ke yawo a kafafen watsa labarai cewa Gwamna Alex Otti na jihar Abia na shirin komawa APC gabanin babban zaɓen 2027.
Ahmad Yusuf
Samu kari