Abdullahi Abubakar
7356 articles published since 28 Afi 2023
7356 articles published since 28 Afi 2023
Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo ya kafa kwamiti mai mutane 14 domin fara binciken tsohuwar gwamnatin jihar karkashin Godwin Obaseki da ta sauka.
An yi rashin fitaccen malami kuma shugaban kungiyar JNI, Jafaru Makarfi a jihar Kaduna a daren jiya Asabar 23 ga watan Nuwambar 2024 yana da shekaru 93.
Sanata mai wakiltar Gombe ta Arewa, Ibrahim Hassan Dankwambo ya sanar da rasuwar tsohon shugaban PDP a karamar hukumar Gombe, Alhaji Idris Bello.
Hadimin Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom, Aniekeme Finbarr a bangaren wayar da kan al'umma ya yi murabus daga mukaminsa domin neman kwarewa a wani sashe.
Kungiyar matasa da suka ci gajiyar N-Power ta shirya gudanar da zanga-zangar kwanaki biyar kan basukan da suke bin gwamnati har na tsawon watanni tara.
Kungiyar Arewa Consultative Forum (ACF) ta yi magan kan masu zargin cewa tana sukar gwamnatin Bola Tinubu saboda dan Kudu ne inda ta ce har Muhammadu Buhari ta soka.
Rahotanni sun tabbatar da mutuwar fitaccen dan siyasa kuma tsohon Sanata a jihar Kano, Aminu Inuwa wanda ya rasu a jiya Juma'a 22 ga watan Nuwambar 2024.
Kanin tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabi'u Kwankwaso ya maka Gwamna Abba Kabir a kotu kan takaddamar fili domin bukatar kotu ta takawa gwamnan birki.
Gwamnonin jam'iyyar PDP sun taru a jihar Plateau domin nemo hanyoyin kawo hadin kai da zaman lafiya a jam'iyyar tare da dawo da martabarta a idon yan Najeriya.
Abdullahi Abubakar
Samu kari