Abdullahi Abubakar
7313 articles published since 28 Afi 2023
7313 articles published since 28 Afi 2023
Gwamna Monday Okpebholo na jihar Edo ya kawo ziyara ta musamman ga Abba Kabir Yusuf domin jajanta masa kan kisan gilla da aka yi wa Hausawa a garin Uromi.
Kungiya ta soki Gwamna Abba Kabir Yusuf da Sarkin Kano Sanusi Lamido Sanusi bisa kin bin umarnin 'yan sanda, wanda ya janyo mutuwar mutane da dama.
Lauya Abba Hikima da sauran lauyoyi da ke kokarin neman hakkin wadanda aka kashe a Edo sun dakatar da shirin zuwa jihar bayan gwamnatin Kano ta kafa kwamiti.
Bayan kammala sallar idi a Gombe, rahotanni sun tabbatar da cewa an samu turmutsutsu yayin da yara biyu suka rasa rayukansu sannan wasu 20 suka jikkata.
Shugaban kasa, Bola Tinubu ya fadi yadda ya yi barazanar korar Minista Nyesom Wike idan manufofinsa ba su dace da bukatun jam’iyyar APC mai mulki ba.
Rundunar ‘yan sandan Kano ta cafke Usman Sagiru mai shekara 20 daga Sharifai kan zargin kashe wani dan sa-kai da harin da aka kai bayan sallar idi a Kano.
Rundunar ‘yan sandan Katsina ta cafke wani mutum, Alhaji Surajo Mai Asharalle da wasu uku kan zarginsu da kai wa jami’an Hisbah hari, inda suka jikkata su.
Yayin da ake bikin sallah a Najeriya, Sheikh Muhammed Habibullah Adam Abdullah El-Ilory ya bayyana Litinin, 31 ga Maris, 2025, a matsayin ranar Eid-el-Fitr.
Bayan kisan ƴan Arewa a jihar Edo, babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya yi Allah wadai da kisan gilla da aka yi wa wasu mafarauta.
Abdullahi Abubakar
Samu kari