Abdullahi Abubakar
7263 articles published since 28 Afi 2023
7263 articles published since 28 Afi 2023
Sarki Muhammadu Sanusi II ya bayyana dalilin da yasa Goodluck Jonathan ya dakatar da cire tallafin man fetur a 2012, yana cewa tsoron harin Boko Haram ne.
Gwamna Dikko Radda ya nada tsohon ministan sufurin jiragen sama, Sanata Hadi Sirika, a matsayin shugaban majalisar gudanarwa ta jami’ar UMYU Katsina.
Jam’iyyar ADC mai adawa a Najeriya ta zargi gwamnatin tarayya da yin amfani da farashin abinci don neman farin jini kafin zaben shekarar 2027 da ke tafe.
Ministan Tsaro, Mohammed Badaru Abubakar, ya umurci sababbin shugabannin rundunonin tsaro su haɗa kai da juna wajen tabbatar da zaman lafiya a ƙasar.
Tsohon Sanatan kaduna ta Tsakiya a Najeriya, Shehu Sani ya ce neman ƙirƙirar sababbin jihohi shekara daya kafin zaben 2027 ba shi da amfani kuma bata lokaci ne.
Tsohuwar matar Sani Danja, Mansurah Isah ta shirya daukar mataki kan wata jaridar yanar gizo bayan wallafa wani rahoton cewa za ta auri Mai Wushirya.
Fasto Ezekiel Dachomo daga jihar Plateau ya ce idan an sace shi, kada a biya fansa, yana mai cewa jinin sa zai haifar da yaki na ’yantar da Kiristoci.
Farashin shinkafa ya fadi sosai a kasuwannin Lagos saboda karin shigo da ita ta iyakoki, lamarin da ya rage wa masu saye ciniki wanda ya jawo faduwarta.
Sakatare Janar na Vatican, Pietro Parolin, ya ce rikice-rikicen tsaro a Najeriya ba na addini ba ne, amma suna da tushe na zamantakewa da ake samu.
Abdullahi Abubakar
Samu kari