Abdullahi Abubakar
7258 articles published since 28 Afi 2023
7258 articles published since 28 Afi 2023
Dangin shugaban IPOB, Mazi Nnamdi Kanu sun ce akwai makirci na kashe shi bayan kotu ta yanke masa hukuncin ɗaurin rai da rai kan tuhumar ta’addanci.
Rahotanni sun tabbatar da cewa an goge shafin Facebook na Fasto Ezekiel Dachomo yayin da ake cece-kuce kan kalamansa game da kisan Kiristoci a Najeriya.
Kotun Tarayya ta karyata labarin cewa an yi yunkurin hallaka Mai Shari'a, James Omotosho saboda hukuncin da ya yanke kan Nnamdi Kanu a makon jiya.
Ministan yada labarai, Mohammed Idris ya bayyana cewa tawagar gwamnati a Amurka na kokarin gyara labaran karya da ke zargin wariyar addini a Najeriya.
Gwamna Zulum ya umurci mazauna Borno su gudanar da azumi da addu’a a Litinin domin neman taimakon Allah kan sabon tashin hankali da ake fuskanta a jihar.
Karamin ministan gidaje, Abdullahi Ata ya mayar da martani ga gargadin APC a Kano, yana cewa maganganunsa ko kusa ba su saba ka'ida da dimokuraɗiyya ba.
Ministan tsaro Bello Matawalle ya ce an kama sojojin da suka janye kafin sace daliban Maga, kuma za su fuskanci hukunci idan aka same su da laifi.
Ministan yada labarai, Mohammed Idris ya ce gwamnati ba ta gurfanar da masu zargin daukar nauyin ta’addanci ba saboda binciken lamuran yana da sarkakiya.
Fasto Elijah Ayodele ya soki Shugaba Bola Tinubu saboda karuwar sace-sace da kashe-kashe, yana cewa idan ya kasa magance tsaro ya kamata ya yi murabus.
Abdullahi Abubakar
Samu kari