Abdullahi Abubakar
7253 articles published since 28 Afi 2023
7253 articles published since 28 Afi 2023
Gwamnan Ebonyi, Francis Ogbonna Nwifuru, ya amince da biyan ₦150,000 a matsayin alawus din Kirsimeti ga dukkan ma’aikatan gwamnati a jihar gaba daya.
Hadimin tsohon shugaban mulkin soja, Janar Yakubu Gowon, Adeyeye Ajayi ya musanta jita-jitar rasuwarsa, yana bayyana ta a matsayin labarin karya.
Fasto Elijah Ayodele ya ce Naira miliyan 150 ba za su iya sayen takalmin da yake sawa ba, yana karyata zargin karɓar kuɗin sihiri daga Bayo Adelabu.
Rundunar ‘yan sanda a jihar Sokoto ta sanar da rasuwar mataimakin kwamishina mai kula da ayyuka, DCP Kabiru Audu wanda ya bar duniya bayan jinya mai tsawo.
Karamin Ministan Tsaro a Najeriya, Dr. Bello Matawalle, ya musanta zargin alaka da yan ta’adda, yana kalubalantar masu zargi su kai shi kotu da hujjoji.
Sabuwar rigima na kunno kai tsakanin bangaren Gwamna Siminalayi Fubara da Ministan Abuja, Nyesom Wike, kan batun rabon mukaman kwamishinoni a Rivers.
Sanata Natasha H Akpoti ta bayyana cewa ba ta da niyyar komawa jam’iyyar APC, duk da tayin da ta ce ana ci gaba da yi mata daga wasu a fadar shugaban kasa.
Majalisar ƙasa ta Austria ta amince da sabuwar doka da ta haramta sanya hijabi ga ’yan mata Musulmai ƙasa da shekara 14 a makarantu wanda ake sukar matakin.
Dan bindiga, Bello Turji ya fito da sabon bidiyo yana karyata zargin cewa Bello Matawalle ya ba ’yan bindiga kuɗaɗe, yana cewa ba a taba ba shi miliyoyi ba.
Abdullahi Abubakar
Samu kari