Wani Fasto Dan shekara 50 yayi ma wata ‘yar yarinya ciki

Wani Fasto Dan shekara 50 yayi ma wata ‘yar yarinya ciki

Abin Kunya: Wani Fasto Dan shekara 50 yayi ma wata ‘yar yarinya budurwa mai shekara 20 ciki.

Wata yarinya ‘yar shekara 21 a duniya ta fasa kwan yadda aka yi wani fasto mai suna Attie Kgware, yayi mata ciki, daga baya kuma ya watsar da ita bayan ta fada masa tana dauke da juna biyu.

Wani Fasto Dan shekara 50 yayi ma wata ‘yar yarinya ciki

 

 

 

 

 

Wata Yarinya mai suna Lekhula, a wata hira da tayi da Jaridar Daily Sun ta bayyana yarda wani limamin coci ya yaudare ta, Fasto Attie Kgware yayi mata alkawarin mota, ya kwanta da ita. Lekhula ta bayyana cewa Faston bai ko yi amfani da bororon roba ba, ya fada mata cewa yafi tsarki a hakan. Lekhula take fada da bakin ta: “Ya fada mani ba sai mun yi amfani da bororon rob aba, domin kuwa shi mutum ne mai tsarki. Zai tsarkake ni da ruwan sa, hakan na yarda domin ina so in samu tsarki a rayuwa.” Lekhula ta ke bayani: “A cocin sa nake ibada, ‘Your choice Christian Ministries’, watan Junairu ya fada mani cewa, saurayi na yana mani surkulle, abin ya daure mani kai. Da yake limamin mu, ma amince da shi, shi kuma yayi amfani da wannan dama ya mani illa. Yayi mani alkawarin motar howa a wancan lokacin, amma yanzu da nake dauke da ciki, bay a son gani na.”

Wani fasto da ke cocin mai suna Vusi Masiya, wani mai harkar saida motoci ya tabbatar da cewa Fasto Kgware ya zo binciken motar da zai siya ma yarinyar, har ma ya tambaye sa ko me ke tsakanin su (Da yar yarinyar), sai dai bai ce komi ba. Ni na san yana da aure, wannan abin kunya ne ga duk wani fasto iri na.

A SAUKE MANHAJAR MU DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMU-DUMI.

Sai dai matar fasto Kgware mai shekaru 47 ta musanta labarin Lekhula, Lekhula dai sakatariyar cocin ce, amma tace mijinta bai taba kwanciya da wata ba, kurum karya ake masa. Amma kuma uwar yarinyar, ta bayyana cewa faston ya zo ya same ta da maganar auren diyar ta. Faston yana fada mata, ya samu matsala a auren sa.

KU KARANTA: UMMARU SHINKAFI YA RASU

 

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng