Shugabancin 2023: Yakasai ya lissafa 'yan siyasa 3 na kudu da ka iya nasara a matsayin dan takarar APC

Shugabancin 2023: Yakasai ya lissafa 'yan siyasa 3 na kudu da ka iya nasara a matsayin dan takarar APC

  • Tsohon hadimin Gwamna Ganduje, Salihu Tanko Yakasai, ya lissafa Tinubu da wasu mutum biyu a matsayin 'yan takarar kujerar shugaban kasa a 2023 na jam'iyyar APC da ka iya nasara daga kudu maso yamma
  • Yakasai ya kuma ce ya kamata yankin kudu maso yamma ya samar da wanda zai gaji shugaba Buhari a 2023, ganin irin gudunmawar da shiyyar ta bayar ga nasarar APC
  • Jigon na APC ya kuma ce zai zama rashin adalci idan wani dan Arewa ya gaji Shugaba Buhari a 2023

Salihu Tanko Yakasai, tsohon hadimin gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya ce dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) yana yankin kudu maso yamma, ba a kudu maso gabas ba.

Tsohon hadimin gwamnan ya yi ikirarin cewa shiyyar kudu maso gabas ba ta da lambar siyasa da kuma dan takarar da ke da karfi don jan kuri'u a fadin kasar a zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan

Da yawa daga cikin masu sukar Buhari su kan lallaɓa Villa diɓar 'jar miya'

Shugabancin 2023: Yakasai ya lissafa 'yan siyasa 3 na kudu da ka iya nasara a matsayin dan takarar APC
Shugabancin 2023: Yakasai ya lissafa 'yan siyasa 3 na kudu da ka iya nasara a matsayin dan takarar APC Hoto: Yemi Osinbajo, Kayode Fayemi, Amb Megarantee
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Yakasai ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a, 24 ga watan Satumba, lokacin da ya bayyana a matsayin bako a gidan talabijin na Arise.

An kori Yakasai wanda ya kasance dan APC a farkon shekarar 2021 saboda sukar shugaban kasa Muhammadu Buhari kan karuwar barazanar tsaro a kasar.

Yakasai ya lissafa wadanda za su iya tsayawa takara daga kudu maso yamma

1. Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo

2. Asiwaju Bola Tinubu

3. Gwamna Kayode Fayemi

Yakasai ya lissafa jiga -jigan APC, wadanda ke da ikon lashe zaben shugaban kasa mai zuwa a matsayin jagoran APC na kasa, Bola Tinubu; Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo gwamnan jihar Ekiti Kayode Fayemi.

Sai dai kuma, tsohon hadimin gwamnan na kafofin watsa labarai, ya ce ba shi da wani dan takara da ya fi so daga kudu maso yamma, Daily Post ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Duk da yi wa Yusuf Buhari fatan mutuwa, shugaba Buhari ya yafewa Fani-Kayode

Dalilin da ya sa ya kamata dan takarar shugaban kasa na APC ya fito daga kudu maso yamma

Yakasai ya kuma bayar da hujjar cewa ya kamata dan takarar shugaban kasa na APC a 2023 ya fito daga kudu maso yamma saboda shiyyar "ta matukar" bayar da gudunmawa wajen kafa jam'iyyar mai mulki.

Ya kara da cewa kudu maso yamma shine "ya ba da mafi girman gudummawa" ga nasarar jam'iyyar da lashe zaben Buhari a 2015.

Ya ce:

"A cikin APC, ya kamata mulki ya karkata zuwa kudu har ma a kudu, ina da ra'ayin dan takarar APC ya fito daga kudu maso yamma kuma ina da dalilina na fadin hakan."

Yakasai ya kuma ce zai zama rashin adalci ne idan wani dan arewa ya gaji shugaba Muhammdu Buhari a 2023.

Ya ce:

“Ba zai yiwu APC ta kasance a kan mulki na tsawon shekaru takwas tare da shugaban kasa dan arewa sannan wani (dan arewa) ya hau mulki ya ci gaba. Wannan zalunci ne."

Kara karanta wannan

Gagarumin sako zuwa Kudu maso Gabas: Ku rungumi APC ko ku rasa dama a 2023, Tsohon dan majalisa yayi gargadi

Shugabancin 2023: Jerin manyan 'yan PDP 3 da za su yi gasar neman tikitin Jam'iyyar

A gefe guda, mun ji cewa yayin da zaben shugaban kasa na 2023 ke karatowa, 'yan siyasa a fadin jam’iyyun siyasa sun fara hararar tikitin jam’iyyarsu domin zama yan takara.

Ga jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), akwai ikirarin cewa manyan sunaye za su sake fitowa kamar yadda aka yi a zaben 2019.

Wasu daga cikin manyan jiga-jigan da ake sa ran za su fafata don neman tikitin takarar shugaban kasa na PDP su ne Bukola Saraki, Atiku Abubakar, da Aminu Tambuwal, duk da cewa har yanzu ba su nuna sha’awarsu a takarar ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel