Ana rade-radin tsohon Ministan Buhari ya tara Naira biliyan 9.7 a lokacin da yake ofis

Ana rade-radin tsohon Ministan Buhari ya tara Naira biliyan 9.7 a lokacin da yake ofis

  • Ana jita-jitar Ibe Emmanuel Kachikwu ya samu biliyoyin kudi da yake Minista
  • Tsohon Ministan na fetur ya karyata wannan zargi, ya bukaci AGF ya yi bincike
  • Dr. Ibe Emmanuel Kachikwu ya aika takardar korafi zuwa ga Abubakar Malami

Tsohon ministan harkokin man fetur, Dr. Ibe Emmanuel Kachikwu ya karyata zargin cewa ya tara Naira biliyan 9.7 a asusunsa a lokacin da yake ofis.

Dr. Ibe Emmanuel Kachikwu ya rubuta takardar korafi zuwa ga Ministan shari’a, kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami SAN.

Jaridar Reuben Abati ta rahoto cewa tsohon Ministan ya rubuta korafi ta hannun lauyansa, Johnmary Jideobi, yana karyata zargin da ake yi masa.

Lauyan Kachikwu ya yi magana

Barista Johnmary Jideobi yace wasu ne kurum suke neman su bata sunan Ibe Emmanuel Kachikwu.

Wata jaridar yanar gizo ta zargi Ibe Kachikwu da mallakar wata mota da aka sato daga kamfanin Jaguar a Birtaniya, aka kai ta California a kasar Amurka.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Jami'in dan sanda ya harbe abokin aikinsa dan sanda a jihar Kano

Tsohon Ministan fetur
Ibe Kachikwu Hoto: www.signalng.com
Asali: UGC

“An kawo wannan rahoto da aka wallafa ne da niyyar bata suna da kimar mutum mai daraja da martaba da muke kare wa, cewa ya dauko motar sata.”
“Bayan labarin ya kasance na karya, amma an wallafa shi ne da nufin bata masa rai, a tada masa hankali, a ci masa mutunci, sannan a bata masa suna.”

Lauyan ya yi kira ga Ministan shari’ar ya yi cikakken bincike a kan wannan korafi da ya gabatar saboda nauyin laifufukan da aka jefi Kachikwu da su.

Johnmary Jideobi yake cewa kowa ya san tsohon Ministan man fetur da daraja da halin kwarya.

Lauyan yace Kachikwu ya rike Minista, shugaban kungiyar GECF, shugaban OPEC da kungiyar APPO baya ga kyaututtuka iri-iri da ya samu a Duniya.

Kara karanta wannan

Yan fashi sun taremu a hanya, sun kwace takardun kotu hannunmu, Lauyoyin DSS ga Alkali

Ana rikici a APC Enugu

Rigingimun cikin gidan jam’iyya sun sa Shugaban APC ya fada hannun ‘Yan Sanda. ‘Yan Sanda sun shiga sakatariyar APC, sun kudunduno Ben Nwoye.

Amma daga baya jami’an tsaro sun fito da Ben Nwoye, kuma ya fadi wanda ya sa aka kama shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel