‘Yan Sanda sun shiga sakatariyar APC, sun kudunduno Shugaban Jam’iyya na riko

‘Yan Sanda sun shiga sakatariyar APC, sun kudunduno Shugaban Jam’iyya na riko

  • ‘Yan Sanda sun je ofishin jam’iyyar APC a Enugu, sun kama Ben Nwoye
  • An yi ram da Dr. Nwoye ne bayan ya gama rantsar da shugabannin APC
  • Shugaban rikon kwaryar yace Ken Nnamani ya kai shi wajen ‘yan sanda

Enugu - Shugaban rikon kwarya na jam’iyyar APC a jihar Enugu, Dr. Ben Nwoye ya na hannun ‘yan sanda. Jaridar Today.ng ta fitar da wannan rahoto.

A ranar Talata, 7 ga watan Satumba, 2021, jami’an ‘yan sanda suka kama Dr. Ben Nwoye a sakamakon wani korafi da Sanata Ken Nnamani ya gabatar.

Rahoton yace tsohon shugaban majalisar dattawan kasar, Ken Nnamani, ya kai karar shugaban rikon kwarya na jihar bayan zaben shugabanni da aka shirya.

Nwoye ya rantsar da shugabannin APC na kananan hukumomi

Kara karanta wannan

Tsohon ‘dan takarar Shugaban kasa ya samu matsayi daga sauya-sheka zuwa APC

Jami’an ‘yan sanda 20 suka dura sakatariyar jam’iyyar APC na Enugu jim kadan bayan Nwoye ya rantsar da sababbin shugabanni na kananan hukumomi 17.

Daily Post tace daga baya an saki shugaban jam’iyyar. Kamar yadda Dr. Nwoye ya shaida wa ’yan jarida, Ken Nnamani ne ya kai kararsa wajen ‘yan sandan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban kasa
Buhari ya na yawon kamfe Hoto: www.politico.ng
Asali: UGC

“Sun kama ni tare da sauran shugabanni. Abin takaici da mu ka isa, sai Kwamishinan ‘yan sanda yace bai san da zaman takardar da tace a kama ni ba.”
“An taso ni gaba kan wasikar da Nnamani ya rubuta. Ya zarge ni da sata, badakala da damfara ta yanar gizo.”

Nwoye yake cewa tsohon shugaban majalisar dattawan ya aika takardar korafi ne da sunan Akpanudoede, yace bai san komai a kan wadannan zargin ba.

“Sun dauki jawabin da na gabatar. Wannan yana cikin shirin da ake yi na kashe jam’iyyar APC. Amma sun fado.”

Kara karanta wannan

Jigon APC ya bayyana wanda ya dace da mulki, ya cire Osinbajo, Tinubu a lissafin 2023

Da manema labarai suka tuntubi mai magana da yawun bakin rundunar ‘yan sandan jihar Enugu, Daniel Ndukwe, ya bayyana cewa bai san an kama Nwoye ba.

Rikici APC ta Legas

Rahotanni sun shaida mana cewa ‘ya ‘yan jam'iyyar APC a jihar Legas suna rigima kan wanda zai rike kujerar shugaban jam’iyya a karamar hukumar Ifako/Ijaye.

Yayin da jigon APC a yankin, Bola Tinubu yake kasar waje, babu zaman lafiya a jam’iyyar mai mulki. Wasu suna zargin ana neman saba yarjejeniyar da aka yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel