Yan fashi sun taremu a hanya, sun kwace takardun kotu hannunmu, Lauyoyin DSS ga Alkali

Yan fashi sun taremu a hanya, sun kwace takardun kotu hannunmu, Lauyoyin DSS ga Alkali

  • An shiga rudani a kotu ranar Laraba, 8 ga Satumba yayinda aka koma zaman hadiman Sunday Igboho
  • Amma Lauyoyin DSS sun ce barayi sun kwace takardun kotu hannunsu yayinda suke hanyarsu ta zuwa kotu
  • DSS ta tuhumi mutum biyu cikin hadiman Sunday Igboho da ta'addanci

Daya daga cikin lauyoyin hukumar tsaron farin kaya DSS, I. Awo, ya bayyanawa kotu cewa yan fashi sun kwace takardar karar da hadiman Sunday Igboho suka shigar kan hukumar.

Lauyan ya bayyana hakan ne a babban kotun tarayya, ranar Laraba, 8 ga Satumba, yayinda aka koma kotu, rahoton Punch.

Lauyan DSS ya bayyanawa Alkali Obiora Egwuatu cewa ya kamata abokin aikinsa ya kawo takardun kotu amma yayi rashin sa'ar shiga cikin motar yan fashi.

Kara karanta wannan

Kashi 55% na nade-naden da Buhari yayi yan kudancin Najeriya ya baiwa, Hadimin Shugaban kasa

Ya kara da cewa yan fashin sun kwace dukkan abubuwan dake hannunsa.

Saboda haka, lauyan ya bukaci Alkalin ya dage zaman.

Yan fashi sun taremu a hanya, sun kwace takardun kotu hannunmu, Lauyoyin DSS ga Alkali
Yan fashi sun taremu a hanya, sun kwace takardun kotu hannunmu, Lauyoyin DSS ga Alkali Hoto: DSS
Asali: Facebook

Sunday Igboho ya ce a mika shi ga Najeriya bai jin tsoron karo da gwamnatin Buhari

Sunday Igboho, ya bayyana kwarin gwiwar samun 'yanci idan Jamhuriyar Benin ta dawo dashi hannun gwamnatin Najeriya.

A cikin faifan sautin da jaridar Punch ta samu wanda kuma majiyoyi da yawa suka tabbatar, Igboho ya ce bai damu da a daure shi kamar yadda aka daure Nnamdi Kanu ba.

Ya yi zargin cewa wasu lauyoyi a jamhuriyar Benin sun karbe kudinsa, kuma sun yaudareshi yayin da suka yi watsi dashi a hannun gwamnatin kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel