Za a gurfanar da masallatai da majami’un da ke amfani da amsakuwa saboda gurbata muhalli da hayaniya – NESREA

Za a gurfanar da masallatai da majami’un da ke amfani da amsakuwa saboda gurbata muhalli da hayaniya – NESREA

  • Hukumar NESREA ta ce akwai masallatai da coci-coci da masana’antun da ke damun jama’a da hayaniyar amsakuwa
  • A cewar Babban Daraktan hukumar, matsalar hanayinar na haifar wa da mutane hawan jini da sauran cututtuka
  • Ya ce dabbobi da tsirrai ma ba su tsira ba daga illar hayaniya

Hukumar tabbatar da inganci da bin dokokin muhalli ta kasa, NESREA, ta ce tana da ikon gurfanar da masallatai da coci-cocin da ke amfani da amsakuwa fiye da kima yayin da suke ibada.

Darakta Janal na hukumar Aliyu Jauro, shi ne ya sanar da haka yayin da yake hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, ranar Lahadi a Abuja.

A cewarsa, hayaniya guda ne cikin muhimman ababuwan da ke gurbata muhalli, yana mai cewa hayaniyar takan shafi ba ma mutane kawai ba, har ma da dabbobi da tsirrai.

Yace:

“Da zarar hayaniyar ta yi wa mutane yawa za ta haddasa wa mutane matsalolin cututtuka kamar hawan jini da dai sauran matsalolin. Don haka, a matsayinmu na hukumar gwamnati muna da ka’idoji na musamman wajen kula da hayaniyar a cikin jama’a.
“Abin da muke yi a nan hukumarmu shi ne mu tabbattar da ana bin dokokin sau da kafa. Akwai ababuwa da dama da mutane ke yi da ke shafar mutane da muhalli. Muna samun korafe-korafe daga wajen jama’a.
“Alal misali, wurare kamar coci-coci da masallatai har ma da masana’antu duk sukan haddasa hayaniya wanda mutane na kawo mana korafi a kai. Don haka muna ziyartar wadannan wuraren domin fadakar da su illar da ke tattare da abin da suke haifar wa jama’a.
“Muna kuma gwada musu yadda za su rika gudanar da ayyukansu ba tare da sun gurbata muhalli da hayayina ba. Muna tabbatar da an bi dokokin da suka dace a duk sands bukatar hakan ta taso,”.

NESREA
Za a gurfanar da masallatai da majami’un da ke amfani da amsakuwa saboda gurbata muhalli da hayaniya – NESREA
Asali: UGC

Mista Jauro ya kuma yi kira ga sauran masu ruwa da tsaki a harkar muhallin da ci gaba da fadakarwa domin kawo karshen matsalar gurbata muhallin a Najeriya.

Ya ce fadakarwar za ta taimaka wa mutane fahimtar illar da ke tattare da haddasa hayaniya cikin jama’a da dabbobi da ma tsirrai da kuma shi kansa muhallin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel