Zulum ya tuhumi shugabar makarantar da ta dakatar da dalibai saboda kin tarbar Buhari

Zulum ya tuhumi shugabar makarantar da ta dakatar da dalibai saboda kin tarbar Buhari

  • An tuhumi shugabar kwalejin da yin gaban kanta wajen dakatar da daliban
  • An ba ta sa’o’i 48 da ta amsa tuhumar
  • Gwamnatin Jihar Borno ta ce matakin shugabar kwalejin ya shafa wa jihar bakin fenti

Kwamishinar Lafiya a Jihar Borno, Juliana Bitrus, ta aika takardar tuhuma ga shugabar Kwalejin Aikin Jinya da Ungozoma Rukaiya Shettima Mustapha, saboda dakatar da wadansu dalibai bisa ikirarin wai sun ki tarbar Shugaba Muhammadu Buhari ranar 17 ga watan Yuni a Maiduguri.

Gwamna Zulum ya bayyana hakan a jawabin da ya saki a shafinsa na Facebook.

Kwamishinar ta bayyana shugabar kwalejin a matsayin wacce ta yi wa gwamnatin Jihar Bornon sharri saboda gaban kanta ta yi wajen daukar matakin ba tare da ta samu umarnin aikata hakan ba ko dai daga gwamnatin jihar ko kuma ma’aikatar.

A takardar tuhumar mai lamba MOH/PER/752 V.I da mai dauke da kwanan watan 25 ga watan Yuni kwamishinar ta bukaci shugabar Kwalejin da ta amsa tuhumar cikin sa’o’i 48 da gamsassun hujjojin dalilin da ya sanya ba za a dauki matakin ladaftarwa a kanta ba.

Ta ce gwamnatin Jihar Borno nada manyan makarantun gaba da sakandaren guda takwas, amma akwai abin daure kai sai a Kwalejin jinya da ungozoman ne kadai za a dakatar da dalibai tare da aika musu da takardun da aka sanya hannu a kai domin kawai a shafa wa gwamnatin jihar kashin kaji.

shugabar makarantar da ta dakatar da dalibai saboda kin tarbar Buhari ta samu tuhuma
Zulum ya tuhumi shugabar makarantar da ta dakatar da dalibai saboda kin tarbar Buhari Hoto: Governor of Borno
Asali: Facebook

Tarban Buhari ba wajibi bane

Kwamishinar ta ci gaba da cewa, koda yake al’ada ce dalibai su fito domin tarbar shugaban kasa idan ya kawo ziyara a ko ina cikin kasar nan, amma ai yin hakan ba wajibi ba ne.

Sannan ko alama daliban ba su kai adadin jama’ar garin da suka yi fitar dango wajen tarbar shugaban kasar daga sassa daban daban na birnin Maiduguri.

Kwamishinar ta ci gaba da cewa ma’aikatar ta gagara fahimtar matakin da shugabar kwalejin ta dauka saboda haka sai da aka dauki lokaci ana binciken lamarin kafin daga bisani aka tuhumi shugabar kwalejin.

Idan za a tuna shugaba Buhari ya kai ziyarar duba halin tsaro a Maiduguri, inda a lokacin ziyarar ya bude rukunin farko na gidaje 10,000 da za a sake tsugunar da. ‘yan gudun hijira a jihar da ma wasu ayyukan da gwamnatin ta gudanar kimanin 550.

Asali: Legit.ng

Online view pixel