An dakatar da dalibai biyu saboda ‘yaga’ Alqur’ani a gaban ’yan uwansu dalibai

An dakatar da dalibai biyu saboda ‘yaga’ Alqur’ani a gaban ’yan uwansu dalibai

• Dalibai biyu a makarantar Fulwood a garin Preston na Ingila sun kai littatafan Alkur’ani biyu makarantar

• Sun muzanta littatafan a gaban ’yan uwansu dalibai

• Makarantar ta dakatar da dukkan daliban biyu sannan ’yan sanda na gudanar da bincike

Daily Mail ta ruwaito cewa an dakatar da daliban wata makarantar sakandare guda biyu bayan da suka ’yaga’ Alkur’ani a gaban wadansu ’yan uwansu daliban.

Malamai sun ankarar da ’yan sanda da jami’an yaki da ta’addanci bayan faruwar lamarin a makarantar Fulwood da ke Preston cikin makon jiya.

Shugaban makarantar Dave Lancaster ya ce ya yi gaggawar sanar da jami’an ’yan sandan garin Lancashire da ma jami’an yaki da ta’addanci domin kare wadannan yaran daga barazanar fadawa tarkon tsaurin ra’ayi.

Dukkan daliban biyu da suka yi danyen aikin muzanta Alkur’anin a gaban ’yan uwansu dalibai an dakatar da su yayin da ake ci gaba da binciken lamarin.

Duk wani matakin da makarantar za ta dauka za a iya sake nazari kansa bayan ’yan sanda sun kammala bincikensu.

An dakatar da dalibai biyu saboda ‘yaga’ Alqur’ani a gaban ’yan uwansu dalibai
An dakatar da dalibai biyu saboda ‘yaga’ Alqur’ani a gaban ’yan uwansu dalibai

Cikin wata wasika zuwa ga iyayen dalibai da aka aika ranar Lahadin nan, Shugaban makarantar, Dave Lancaster ya ce "ba manufarmu ba ce mu kawar da ido kan irin wadannan ayyukan sannan za mu tabbatar wa kowa cewa za mu ci gaba da aiki tare wajen karfafa tsarin kare makarantarmu sannan mu kara himmatuwa wajen nuna daidaito da tsakanin mabanbantan al’ummomi."

‘’'Yayin da muke ganin akwai hukuncin da lallai za a dauka kan daliban nan, yana da muhimmanci mu gano dalilan da suka sanya daliban suka aikata abin nan wand aba mu taba ganin kwatankwacinsa ba a makarantar nan.

'Ba za mu yi hakan ba mu kadai. Muna aiki tare da ’yan sanda sannan mun riga da mun tuntubi dukkanin hukumomin da suka dace mu tuntuba.

'Dadin dadawa kuma, mun kuma tuntubi Limaman garin domin neman taimakonsu wajen yadda za mu tunkari lamarin," ya kara.

Wani jami’in hulda da jama’a na ’yan sandan garin nan Lancashire ya ce suna sane da faruwar wadannan batutuwan guda biyu da suka faru a makon jiya sannan suna aiki tare da hukumomin makarantar domin shawo kan lamarin

Asali: Legit.ng

Online view pixel