Cikin wata 5, gwamnatin nan ta kashe ’yan kabilar Ibo 513, ta kame 2,436, 854 sun yi batan dabo: Ohanaeze

Cikin wata 5, gwamnatin nan ta kashe ’yan kabilar Ibo 513, ta kame 2,436, 854 sun yi batan dabo: Ohanaeze

  • Kungiyar Ohanaeze Ndigbo tayi Alla-wadai da kalaman Buhari
  • Sakataren kungiyar yace babu wani kwaskwarimar da za a yi wa kalaman domin sanyaya ran al’ummar Ibo
  • Hakazalika ya ce shugabannin Arewa suna farin ciki da kalaman Shugaba Buhari

Uwar kungiyar ’yan kabilar Ibo, Ohanaeze Ndigbo ta kasa da kasa ta yi Allah wadai da kasa yin magana a kan zargin ci gaba da mayar da al’ummar Ibo saniyar ware da dattawan yankin Arewa suka yi.

Cikin wata sanarwa dauke da sa hannun sakataren kungiyar Okechukwu Isiguzoro a ranar Talata, kungiyar ta yi kakkausar suka kan kalaman da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi cewa inda ya kwatanta ‘kungiyar IPOB da cewa ba ta wuce cikin cokali ba’.

A ranar Alhamis din makon jiya, Shugaba Buhari ya yi barazanar gwamnatinsa za ta aika jami’an soja da na ’yan sanda yankin Kudu maso Gabas domin farautar ’yan haramtacciyar kungiyar IPOB masu neman kafa kasar.

Ya kwatanta kungiyar IPOB tamkar da “dan digo a cikin da’ira wacce ba ta da wata mabuya. Akwai mambobinta da ma kadarorinta warwatse a ko ina.

“Ba su san me suke yi ba sam. Yadda za mu magance su shi ne mu aika da jami’an ’yan sanda da na soja domin su fatattake su," yace.

Har wa yau, Shugaba Buhari ya soki masu kiran kafa ’yantacciyar kasar Biafra da Jamhuriyar Oduduwa, yana mai cewa jahilai ne.

Ohanaeze tayi kuka
Cikin wata 5, gwamnatin nan ta kashe ’yan kabilar Ibo 513, ta kame 2,436, 854 sun yi batan dabo: Ohanaeze
Asali: Getty Images

Sai dai a martaninta, kungiyar ta Ohanaeze ta kwatanta kalaman na Shugaba Buhari a matsayin annoba.

Tana mai cewa 'babu wani kanikancin da za a yi wa kalaman nasa domin sanyaya ran al’ummar Ibo'.

Kungiyar ta bayyana cewa gum da bakin da shugabannin Arewa suka yi kan kalaman ya nuna suna maraba da matsayar Shugaban Kasar kan yankin na Kudu maso Gabas.

Sakataren kungiyar Ibon ya ce ’yan kabilar Ibon kwararru ne a kowane yanayi suka tsinci kansu ciki kuma za su kasance dan hakkin da zai tsone idon dukkanin masu Fir’aunanci kan al’ummar.

Sanarwar ta ce: “Kungiyar Ohanaeze Ndigbo ta duniya baki daya ta kalubalanci shugabannin yankin Arewa da su fito su magana kan kalaman batanci da cin fuskar al’ummar Ibo da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi masu cike da raba kan al’ummar kasa inda ya kwatanta yankin Kudu maso Gabas din a zaman yankin da ke a garkame ta kowace fuska, tana mai cewa babu wani kanikancin da za a yi wa kalaman Shugaban domin sanyaya ran al’ummar Ibon.

‘’A halin yanzu cikin kwana 160, an kashe al’ummar Ibo mutum 513 wadansu 2,436 kuma an kame su yayin da wadansu 854 suka yi batan dabo sakamakon kalubalen tsaron da ake fama da shi a yankin Kudu maso Gabas.’’

Asali: Legit.ng

Online view pixel