Saniyar Ware: Igbo za su sarara idan aka basu Shugaban Kasa a 2023, Ngige

Saniyar Ware: Igbo za su sarara idan aka basu Shugaban Kasa a 2023, Ngige

  • Kundin Mulkin da gwamnatin Abacha ta samar a 1995 shi ne mafi dacewa da ’yan Najeriya
  • ’Yan kabilar Ibo suna da tunanin an mayar da su saniyar ware
  • Tsarin Mulkin 1999 ba shi ne mafita ga shiyyoyin kasar nan ba

Ministan Kwadago da Samar da Ayyuka Dokta Chris Ngige ya bayyana cewa tunanin da al’ummar Ibo na cewa ana take hakkinsu tare da mayar da su saniyar ware a harkokin mulkin kasar nan, zai kau ne kawai idan har Shugaban Kasa na gaba ya fito daga kabilar.

Koda yake, ya fada a wani shirin al’amuran yau da kullum na gidan telebijin din Channels mai taken Newsnight cewa abin bakin ciki a nan shi ne yadda babu wata ayar doka a cikin Kundin Mulkin 1999 da ta ce lallai ne Shugaban Kasa na gaba ya fito daga yankin Kudancin kasar nan.

Ya kara da cewa, wannan shi ne dalilinsa cewa Kundin Mulkin 1995 da gwamnatin marigayi Janal Sani Abacha ya samar shi ne kundi mafi dacewa da yanayin da Najeriya ta tsinci kanta ciki.

Saniyar Ware: Igbo za su sarara idan aka basu Shugaban Kasa a 2023, Ngige
Saniyar Ware: Igbo za su sarara idan aka basu Shugaban Kasa a 2023, Ngige
Asali: Facebook

Yace:

“Mutanen yankin Kudu maso Gabas suna jin cewa an mayar da su saniyar ware kuma ba a yaba wa da himmarsu, ko dai ana fadar hakan saboda farfaganda ko kuma da manufar juya tunanin mutane, a yanzu ba ta wannan batun ake yi ba.
“Don haka na yarda da wannan tsarin, sai dai kash! Kundin mulkin Najeriya bai tanadar da hakan ba. A kan wannan batun ina da ja da wadanda suka samar da Kundin Mulkin na 1999.
“Har yau har gobe ina da amanna a kan Kundin Mulkin 1995 da Abacha ya samar wanda ya yi tanadin karba-karbar shugabanci kasa na sheakar biyar a wa’adi guda tsakanin shiyyoyin siyasar kasar nan guda shida domin magance matsaloIin kama daga nay akin basasa da soke zaben 12 ga watan Yuni.

Yace wannan tsarin mulkin da zai zama na shi ne mafi kyau da dacewa ga ’yan Najeriya nan da shekara 30 masu zuwa inda kowace shiyya za ta dana mulkin kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel