Haramta Twitter: Najeriya tayi asarar kimanin N24.72bn cikin kwanaki 10

Haramta Twitter: Najeriya tayi asarar kimanin N24.72bn cikin kwanaki 10

  • A kowani sa'a daya Najeriya tana asarar kimanin Naira Miliyan 102.9 kimanin Dala 250,600 a dalilin haramci da aka sanyawa kafan sada zumunta na Twitter
  • Twiter ta kasance daya daga cikin shafukan zumunta wanda hada hadan kasuwanci ke gudana
  • Kamfanin sadawar yace a shirye yake domin samun zaman tattaunawa da mahukunta Najeriya

Najeriya ta yi asarar N24.72bn ($ 60.14m) a cikin kwanaki 10 saboda haramcin hana amfani da Kafar sada Zumunta na Twitter a inda dokar ta fara aiki a ranar 5 ga Yuni.

Dangane da NetBlocks Cost of Shutdown Tool, Najeriya na asarar N102.9m ($ 250,600) kowane sa'a sakamakon haramcin.

Gwamnatin Tarayya a ranar 4 ga Yuni, 2021 ta sanar da dakatar da Twitter a Najeriya.

Ministan Yada Labarai da Al’adu, Lai Mohammed, ya bayyana ‘dagewar amfani da dandalin saboda ayyukan da za su iya lalata kasancewar kamfanonin Najeriya’ a matsayin dalilin dakatarwar.

Haramta Twitter: Najeriya tayi asarar kimanin N24.72bn cikin kwanaki 10
Haramta Twitter: Najeriya tayi asarar kimanin N24.72bn cikin kwanaki 10
Asali: UGC

A cewar wani rahoto da Statista ta fitar, Najeriya na da kimanin masu amfani da shafukan sada zumunta kimanin miliyan 33, tare da kimanin kashi 26 cikin 100 a shafin na Twitter.

Lokacin da aka tambaye shi meye hadin haramcin ga harkokin kasuwanci a cikin kasar, Darakta Janar na Nigeria kungiyar Cinikayyar Kasuwanci, Masana’antu, Ma’adanai, da Aikin Gona ta Najeriya, Ayoola Olukanni, sai ya ce,

“Sadarwa muhimmiyar ɓangare ce ta tallace-tallace da kasuwanci a wannan zamani na kwamfuta.
Sakamakon haka, haramcin Twitter zai iya yin tasiri mara kyau kuma wajen dagula harkokin kasuwanci musamman Masana'antu, kanana da matsakaitan Masana'antu wadanda suka dogara da kafofin sada zumunta, kamar Facebook, Instagram gami da Twitter don gudanar da kasuwanci.
“Duk da cewa ana iya la’akari da cewa akwai wasu dandalin sada zumunta, yanayin dakatarwar na nufin rasa abokan hulda da ake da su da kuma samun masu yin hijira.

Kamfanin na Twitter ya bayyana wa gwamnati cewa a shirye take ta hadu don tattaunawa domin magance damuwar juna da ganin an dawo da aikin. Kamfanin ya bayyana hakan ne a cikin wani sakon Tweeter.

Mercy Omohoro, wata ma’abociyar amfani da shafin Twitter kuma yar kasuwa a manhajar, ta ce, “Gaskiya, babu tamkar twitter. A twitter na fara kasuwanci, sannan na yadu zuwa Instagram yan watannin baya kuma na kasa samun damar amfani da dandalin da kyau.

“Ina siyar da gashin kari kuma farcen kari, Ina gab da kaddamar da wani sabon samfuri lokacin da hanin ya faru. Nashiga rudani. ”

Asali: Legit.ng

Online view pixel