Rikicin kabila ya sake barkewa a Gombe, an kona gidaje akalla 50

Rikicin kabila ya sake barkewa a Gombe, an kona gidaje akalla 50

Gwamnatin jihar Gombe a ranar Litnin ta sanar da cewa rikici tsakanin Shongom da Faliya kan filin gona ya yi sanadiyar mutuwar mutum guda tare da kona gidaje akalla 50.

Kwamishanan labaran jihar, Julius Ishaya, ya sanar da hakan a hira da manema labarai bayan zaman majalisar tsaro na Gombe, rahoton Vanguard.

A jawabinsa, ya ce rikicin ya auku ne ranar Asabar, 29 ga Mayu kuma wata mata ta rasa rayuwarta.

"Majalisar tsaro ta jaddada haramta ayyukan yan banga da kungiyoyin mafarauta kuma an sanar da dukkan hukumomin tsaro kan haka," yace.

Ya ce gwamnatin jihar ta umurci shugabannin gargajiyan garuruwan su gana da matasansu domin takaita wannan rikici.

Rikicin kabila ya sake barkewa a Gombe, an kona gidaje akalla 50
Rikicin kabila ya sake barkewa a Gombe, an kona gidaje akalla 50
Asali: UGC

Hakazalika kwamishanan tsaro na jihar, Adamu Dishi, ya ce kurar ta kwanta yanzu.

Ya ce an umurci jami'an tsaro su fito da wadanda suka haddasa wannan rikici, saboda rikici ba ta barkewa da kanta kuma wajibi ne a hukuntasu.

Kwamishanan yan sandan jihar Gombe, Ishola Babaita, ya tabbatarwa kamfanin dillancin labarai NAN wannan labari na rikici tsakanin Shongom da Filiya.

Ya tabbatar da cewa an kona akalla gidaje 50 kuma an hallaka mutum daya.

Ya ce za'a hukunta dukkan wadanda ke da hannu cikin wannan rikici bayan kammala bincike.

Asali: Legit.ng

Online view pixel