Kada Ku Sare Saboda Mutuwar Janar Attahiru: CDS Ga Rundunonin Sojin Najeriya

Kada Ku Sare Saboda Mutuwar Janar Attahiru: CDS Ga Rundunonin Sojin Najeriya

- Babban hafsan hafsoshin tsaro ya bukaci jami'an sojin Najeriya da su ci gaba da aiki tukuru

- Ya ce kada su bari mutuwar shugabansu ya jefa su cikin mummunan alhinin a aikinsu na kasa

- Hakazalika shugaba Buhari ya bayyana cewa, mutuwar shugaban na soji ya kawo ci baya ga kasa

Babban hafsan hafsoshin tsaro, Janar Lucky Irabor a ranar Litinin ya umarci sojoji da su daina jin zafi game da mutuwar Shugaban hafsan sojoji, Laftana-Janar Ibrahim Attahiru da wasu jami’ai 10 a wani hatsarin jirgin sama a Kaduna ranar Juma’a.

Da yake jawabi a gidan Attahiru da ke Abuja yayin addu’o’in kwana uku na Fidau, CDS ya bukaci sojojin su ci gaba da kasancewa masu kwarin gwiwa tare da mai da hankali kan matsayinsu na tsarin mulki, Daily Trust ta ruwaito.

“Sako na ga mambobin rundunar sojojin Najeriya shi ne cewa su ci gaba da jajircewa tare da kwazo kan matsayin su na tsarin mulki a wannan lokacin jarrabawa. Bai kamata karsashinsu yayi sanyi ba game da lamarin da ya faru,'' inji Irabor.

KU KARANTA: Jami'an Tsaro Sun Dakile Yunkurin Kone Ofishin 'Yan Sanda, Sun Kame 'Yan Ta'adda 12

Kada Ku Kwarin Gwiwarku Ya Ragu Saboda Mutuwar Hanar Attahiru: CDS Ga Rundunonin Sojin Najeriya
Kada Ku Kwarin Gwiwarku Ya Ragu Saboda Mutuwar Hanar Attahiru: CDS Ga Rundunonin Sojin Najeriya Hoto: guardian.ng
Asali: Facebook

Daraktan Harkokin Addinin Musulunci na Sojojin Najeriya, Birgediya-Janar Shehu Garba Mustapha, wanda ya jagoranci addu'o'in, ya nemi taimakon Allah game da halin rashin tsaro a Najeriya.

Ya kuma yi addu'ar Allah Ya ba shugabannin Najeriya hikima da kwarin gwiwar gudanar da al'amuran kasar nan.

Ya kuma yi addu'ar Allah ya jikan wadanda suka rasu sannan ya ba iyalansu hakurin jure rashin.

A gefe guda, Shugaba Muhammadu Buhari ya yi magana game da mutuwar jami'an, yana mai takaicin cewa hakan ya kawo ci baya a yakin da gwamnatinsa ke yi da rashin tsaro, The Nation ta ruwaito.

KU KARANTA: Gwamna a Najeriya: Ba Na Karbar Albashi a Matsayi na Gwamna, Aiki Kawai Nake

A wani labarin, Misis Dolapo Osinbajo, matar Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo, ta kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan jami’an sojin da suka mutu a hadarin jirgin sama a ranar Juma’a 21 ga Mayu, a Kaduna.

Babban hafsan sojan, Ibrahim Attahiru, tare da wasu hafsoshin sojan 10 sun rasa rayukansu a hadarin jirgi.

Wata sanarwa da Ofishin Mataimakin Shugaban ya aike wa Legit.ng ta nuna cewa Misis Dolapo, nan da nan da jin labarin hadarin, ya sanya ta kai ziyarta ga iyalan jami’an soja da suka mutu, tare da jajanta musu da danginsu, tare da taya su jimamin babban rashin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.