APC ta yi babban rashi yayin da tsohon shugaban jam'iyyar da wasu mambobi 150 suka koma PDP a Abuja

APC ta yi babban rashi yayin da tsohon shugaban jam'iyyar da wasu mambobi 150 suka koma PDP a Abuja

- Tsoffin ‘yan jam’iyyar APC sun nuna rashin jin dadin su ga jam’iyyar mai mulki

- Yan siyasan sun bayyana wasu daga cikin dalilan da suka sa suka sauya sheka zuwa PDP

- Har yanzu APC ba ta mayar da martani ba game da ficewar mambobinta a yankin Kuje da ke Abuja

Godwin Poyi, tsohon shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a yankin karamar hukumar Kuje da ke babban birnin tarayya (FCT) ya sauya sheka zuwa jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Jaridar Vanguard, ta ambaci kamfanin dillacin labarai na Najeriya (NAN), ta ruwaito cewa dan siyasan ya jagoranci mambobi sama da 150 zuwa PDP a ranar Litinin, 24 ga watan Mayu.

KU KARANTA KUMA: Ina kula da su kuma ina biya masu dukka bukatunsu: In ji matar da ta auri maza 7 a cikin wani bidiyo

APC ta yi babban rashi yayin da tsohon shugaban jam'iyyar da wasu mambobi 150 suka koma PDP a Abuja
APC ta yi babban rashi yayin da tsohon shugaban jam'iyyar da wasu mambobi 150 suka koma PDP a Abuja Hoto: @seyiamakinde
Asali: Twitter

Rahotanni sun ce wadanda suka sauya shekar sun mika katunansu na kasancewa mambobin APC, tsintsiya, da fastoci don maye gurbinsu da lema ta jam’iyyar PDP.

A cewarsu, sun yanke shawarar komawa PDP ne saboda ba su gamsu da yadda ake tafiyar da manufofin APC a yankinsu ba.

KU KARANTA KUMA: Bakin ciki da tashin hankali a Benuwe yayin da Makiyaya suka kashe Manoma sama da 100 a garuruwa 4

Godwin Poyi ya ce:

“Mun yanke shawarar komawa PDP ne domin bayar da gudummawa ga ci gaban yankin Kuje da kuma kasar baki daya.

“Ba a karfafawa zaman mu a APC gwiwa ba. Manufofin APC da tsarinta ba su karfafa dimokiradiyya da shugabanci a karamar hukumar ba."

Wadanda suka sauya shekar daga APC sun samu tarba daga shugaban PDP a karamar hukumar Kuje, Ismaila Mohammed.

Jigon na PDP ya ce har yanzu wasu masu sauya sheka na zuwa jam'iyyar don ci gaban dimokiradiyya a Kuje.

A wani labarin, Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike a ranar Litinin, 24 ga watan Mayu, ya ce idan ya fice daga jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) jam’iyyar siyasar za ta wahala.

Daily Trust ta rahoto cewa Wike yayi wannan magana ne kasa da mako guda bayan Gwamna Ben Ayade ya sauya sheka zuwa APC.

Gwamnan yayin ganawa da manema labarai a gidan gwamnati, a Fatakwal, ya yi alfahari game da abin da jam'iyyar adawa za ta fuskanta idan ya yanke shawarar barin cikinta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel