Abubuwa 7 da ya kamata ka sani a kan rayuwar Shugaban sojojin kasa da ya rasu a jirgin sama

Abubuwa 7 da ya kamata ka sani a kan rayuwar Shugaban sojojin kasa da ya rasu a jirgin sama

A ranar Juma’a, 21 ga watan Mayu, 2021, labari maras dadi ya karada Najeriya, inda aka ji rasuwar hafsun sojojin kasa, Ibrahim Attahiru.

Laftana Janar Ibrahim Attahiru ya rasu ya na da shekara 54 a Duniya a sakamakon hadarin jirgi, ya rasu ne tare da mai dakinsa, Hajiya Fati Attahiru.

Ana zargin jirgin saman da ya dauko marigayin da wasu tawagarsa ya gamu da matsala ne bayan an samu matsalar hatso, yayin da gari ya turnuke.

A yau Legit.ng ta tattaro maku kadan daga cikin tarihin Marigayi Janar Ibrahim Attahiru.

KU KARANTA: Buhari ya yi ta'aziyyar COAS, Janar Ibrahim Attahiru

1. An haifi Laftana Janar Ibrahim Attahiru a ranar 10 ga watan Agustan 1966, ya bar Duniya ya na da shekara kusan 55. Asalinsa mutumin jihar Kaduna ne.

2. Attahiru ya na cikin ‘Yan aji na 35 da su kayi karatu a makarantar sojan NDA. An kaddamar da shi bayan ya kammala karatu a matsayin Laftanan a 1986.

3. Janar Ibrahim Attahiru ya taba zama shugaban dakarun Operation Lafiya, Dole da aka kafa domin su yi maganin Boko Haram a yankin Arewa maso gabas.

4. Bayan ‘yan kwanaki shugaban hafsun sojin kasa na lokacin, Laftana Janar Tukur Buratai ya tsige Ibrahim Attahiru bayan ya gaza kamo Abubakar Shekau.

KU KARANTA: Jawabin karshe da Ibrahim Attahiru ya yi

Abubuwa 7 da ya kamata ka sani a kan rayuwar Shugaban sojojin kasa da ya rasu a jirgin sama
Tsohon shugaban sojojin kasa Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

5. Janar Nicholas Rogers ne ya canji Ibrahim Attahiru a Operation Lafiya, Dole. Jaridar Daily Trust ta ce ya rike mukamai da yawa a gidan sojan Najeriya.

6. Kafin ya zama shugaban hafsun sojoji na kasa, shi ne ke rike a bataliyar sojoji ta 82. A ranar 27 ga watan Junairu, 2021, ya zama sabon shugaban sojojin kasa.

7. A ranar Juma’a Ibrahim Attahiru ya rasu tare da wasu mutane kimanin takwas a jirgin sama. Shi ne shugaban hafsun sojan kasa na biyu da ya mutu a jirgin sama.

Kun ji cewa hadarin jirgi ne ya yi sanadiyyar mutuwar Laftana Janar Ibrahim Attahiru. Babban Sojan ya cika ne sa'o'i kadan da jin labarin mutuwar Abubakar Shekau.

Juma'ar jiya bata yiwa Najeriya dadi ba yayin da shugaban hafsoshin Sojin kasan Najeriya, Laftanan Janar Ibrahim Attahiru, ya mutu tare da wasu yaransa a soja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel