Buhari ya fada jimami, ya nuna damuwarsa tare da ta'aziyyar Janar Attahiru

Buhari ya fada jimami, ya nuna damuwarsa tare da ta'aziyyar Janar Attahiru

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana jimaminsa da alhininsa kan mutuwar shugaban rundunar sojin kasa ta Najeriya

- Buhari yayi addu'ar gafara ga rayukan shugaban sojin da kuma hafsoshin sojin da suka rasu a hatsarin jirgin saman

- Ya tabbatar da cewa rayukan masu kishin kasan ba zai tafi a haka ba ballantana lokacin da ake matukar bukatarsu

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiga matukar damuwa a kan hatsarin jirgin sama da yayi ajalin shugaban dakarun sojin kasa, Laftanal Janar Ibrahim Attahiru da wasu manyan sojoji.

Kamar yadda mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya bayyana alhinin da shugaban kasan ya shiga.

"A yayin addu'a ga Ubangiji da ya gafartawa rayukan masu kishin kasan, shugaban kasan yace wannan babban rashi ne yayin da dakarun sojin kasar nan suka zage wurin ganin karshen kalubalen tsaron da kasar nan ke fuskanta," Shehu ya wallafa.

KU KARANTA: Da duminsa: Sojoji sun dira a Oshodin Legas, sun ragargaza ababen hawa masu yawa

Buhari ya fada jimami, ya nuna damuwarsa tare da ta'aziyyar Janar Attahiru
Buhari ya fada jimami, ya nuna damuwarsa tare da ta'aziyyar Janar Attahiru
Asali: Getty Images

KU KARANTA: Dalla-dalla: Yadda Shekau ya sheka lahira tare da wasu kwamandojin ISWAP

Shugaban kasan ya sha alwashin cewa rayukan zakakuran sojin ba zai tafi a haka ba.

Legit.ng ta ruwaito cewa, labari ya na zuwa mana cewa shugaban hafsun sojojin kasa na Najeriya, Laftana Janar Ibrahim Attahiru ya rasu dazun nan.

Mabanbantan rahotanni sun tabbatar mana da mutuwar babban sojan kasar wanda ya shiga ofis a karshen Junairun 2021.

Majiyar ta ce jirgin da ya dauko Janar Ibrahim Attahiru zuwa garin Kaduna ya gamu da hadari a filin sauka da tashin jirage.

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo kasar Najeriya bayan tafiyar da yayi domin halartar muhimmin taro a birnin Paris na kasar Faransa, kamar yadda hadimin shugaban kasan Bashir Ahmad ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Shugaban kasan ya iso kasar wurin karfe 5:15 na yammacin ranar Alhamis inda ya sauka a filin sauka da tashin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe dake garin Abuja.

Idan zamu tuna, Buhari ya sauka garin Abuja a ranar Lahadi zuwa birnin Paris, inda ya kwashe kwanaki hudu domin halartar gagarumin taron farfado da tattalin arzikin Afrika bayan annobar Korona.

Asali: Legit.ng

Online view pixel