Jawabin karshe da Laftanal Janar Attahiru yayi wa dakarun sojin Najeriya

Jawabin karshe da Laftanal Janar Attahiru yayi wa dakarun sojin Najeriya

- An bukaci hukumar hulda da jama'a ta sojin kasa da su inganta ayyukansu

- Wannan ne sakon karshe da marigayi Janar Ibrahim Attahiru ya mika ga sojin

- Janar Ibrahim Attahiru ya rasu sakamakon hatsarin jirgin sama a jihar Kaduna

Shugaban rundunar sojin kasa, Laftanal Janar Ibrahim Attahiru yayi kira ga sojojin kasa dake bangaren hulda da jama'a a kan bukatar inganta ayyukansu na yada labarai.

Yayi wannan kiran ne a ranar Laraba, 19 ga watan Mayun 2021 yayin bude wani taron kwanaki uku na horar da hafsoshi soji dake fanni hulda da jama'a da yada labarai a Abuja.

KU KARANTA: Da duminsa: Kamfanin rarrabe wutar lantarki ya dawo da wutar jihar Kaduna

Jawabin karshe da Laftanal Janar Attahiru yayi wa dakarun sojin Najeriya
Jawabin karshe da Laftanal Janar Attahiru yayi wa dakarun sojin Najeriya
Asali: Getty Images

KU KARANTA: Da duminsa: Sojoji sun dira a Oshodin Legas, sun ragargaza ababen hawa masu yawa

Shugaban rundunar sojin kasa wanda ya samu wakilcin Manjo Janar Ben Ahanotu a taron, yace ya zama dole a yi dubi da kalubalen tsaron da kasar nan ke fuskanta.

Hakan kuwa yana bukatar ingantattun hanyoyin yada labarai domin hakan zai sa a cimma babbar nasara wurin shawo kan matsalolin tsaro.

Yayi kira ga jami'an hulda da jama'a da su kasance a ankare da hakkokin da suke kansu kuma su kasance masu baiwa rundunar kariya. Ya kara da nuna takaicinsa da yadda wasu marasa kishin kasa ke kokarin ganin sun bata kokarin dakarun.

A wani labari na daban, Abubakar Shekau, shugaban kungiyar Boko Haram ya sheka lahira yayin wata arangama da mayakan kungiyar ta'addanci ta ISWAP kamar yadda rahotanni suka bayyana.

A yayin bayyana wani bayanin sirri, Daily Trust ta ruwaito yadda shugaban kungiyar miyagun ta Boko Haram ya rasa rayuwarsa bayan musayar wuta da mayakan ISWAP.

A wani rahoton yadda lamarin ya faru, HumAngle ta ruwaito cewa wasu kwamandojin ISWAP sun rasa rayukansu tare da Shekau.

Hakazalika, jaridar tace a ranar Laraba ne mayakan ISWAP sun kutsa dajin Sambisa a motocin yaki, yankin da marigayi Shekau ya mamaye kuma suka tirsasa Shekau da ya mika kansa bayan an fi karfin dakarunsa.

An gano cewa sun bukaci Shekau da yayi mubaya'a amma yace gara ya kashe kansa da yayi hakan, lamarin kuwa da ya faru.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng