Rikici da Falasdinawa: Kamfanonin jirage sama 7 sun dakatad da zuwa Isra'ila

Rikici da Falasdinawa: Kamfanonin jirage sama 7 sun dakatad da zuwa Isra'ila

Rikicin dake gudana tsakanin kasar Isra'ila da Falasdin ya tilastawa kamfanonin jiragen sama dakatad da zuwa kasar Yahudawan yayinda ake kira ga kasashen duniya su sanya baki.

A cewar AFP, Kawo ranar Alhamis, akalla kamfanonin jiragen kasashe bakwai sun sanar da cewa jiragensu zasu daina zuwa Izra'ila.

Ga jerinsu:

1. KLM

Kamfanin KLM na kasar Holland ya dakatad da zuwa Isra'ila a yanzu, tashar NOS ta bayyana.

2. BA, Virgiin

Kamfanin kasar Birtaniya ya dakatad da dukkan jiragen da suka shirya zuwa Tel Aviv ranar Alhamis, hakazalika kamfanin Virgiin Atlantic ranar Alhamis a Juma'a.

3. Lufthansa

Kamfanin Lufthansa na kasar Jamus ya sanar da cewa "muna sa ran komawa tashi zuwa Isra'ila ranar Asabar, 15 ga Mayu."

4. Aeroflot

Rikici da Falasdinawa: Kamfanonin jirage sama 7 sun dakatad da zuwa Isra'ila
Rikici da Falasdinawa: Kamfanonin jirage sama 7 sun dakatad da zuwa Isra'ila Photo by EMMANUEL DUNAND / AFP)
Asali: UGC

5. Iberia

Kamfanin jirgin na kasar Spain ya fasa tafiyar da yayi niyya zuwa Isra'ila na ranar Alhamis da kuma Asabar.

Wata mai magana da yawin Iberia ta bayyanawa AFP cewa " Zamu yanke shawara kan yadda abubuwa zasu kasance dangane da yadda abubuwa suka kasance."

6. Kamfanin jirgin US

Kamfanonin jiragen AMurka akalla 3; United, Delta da American Air sun dakatad da jiragensu daga zuwa Isra'ila.

7. LOT

Kamfanin jirgin na kasar Poland ya "dakatad da zuwa Isra'ila a yanzu". Kakakin kamfanin Krzysztof Moczulski ya ce: "Ina tunanin ba zamu je na da wasu kwanaki ba."

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng