Bana iya numfashi: Ku taimakawa Rokibat a magance wata bakuwar cuta dake cin fuskarta

Bana iya numfashi: Ku taimakawa Rokibat a magance wata bakuwar cuta dake cin fuskarta

A bayyane yake idan aka ce rayuwa ta sauya mata salo, ciwo ne ke cin ta a cikin shekaru mafi muhimmanci na rayuwarta. Rokibat Adefabi na rayuwa ne a wani lalataccen gidan gado inda burikan ta na rayuwa ke wucewa a kowanne lokaci.

Lamarin ya fara ne 2008 a jihar Legas inda Rokibat ke rayuwa tare da mahaifinta wanda ke aiki a bangaren shari'a.

Kamar yadda tace, ciwonta ya fara ne daga dan karamin kurji da ya fito mata a hanci yayin da take makarantar kwana.

Bayan mahaifinta ya gani, an fara bata magani amma sai kurjin ke girma kuma yana cigaba da yin matsanancin ciwo inda daga bisani aka mika ta asibiti.

Rokibat da mahaifinta sun je asibitin jam'iar koyarwa ta jihar Legas (LASUTH) inda aka basu shawarar komawa asibitin jami'ar koyarwa na Ibadan (UCH).

Bana iya numfashi: Ku taimakawa Rokibat a magance wata bakuwar cuta dake cin fuskarta
Bana iya numfashi: Ku taimakawa Rokibat a magance wata bakuwar cuta dake cin fuskarta
Asali: Original

An mayar da su asibitin UCH a 2009, wannan shine tushen matsalar da karamar yarinyar a lokacin ta fara shiga.

Rokibat ta sanar da wakilin Legit.ng cewa: "A UCH, an mika ni sashin ANT inda aka dinga min gwaje-gwaje na shekara daya. Daga baya an kwantar dani inda aka ce zan dauka tsawon shekaru 4.

"Abun mamakin shine yadda idan an yi magani yau na samu sauki, gobe matsanancin ciwon ne ke dawowa. Daga baya sun sallame ni inda suka ce in dinga zuwa lokaci bayan lokaci."

A 2016, an tura Rokibat sashin MPO a UCH, Ibadan. An bata wani man shafawa saboda ciwon yana cin fuskarta kuma bata iya fita wasa da sa'o'inta.

Mahaifinta ya ziyarci gidajen rediyo biyu inda suka samu tallafin N700,000 wanda aka fara mata magani. Bayan watanni da jin saukinta, mahaifin Rokibat ya rasu.

Bayan rasuwar mahaifin Rokibat, ta koma Iseyin wurin kakarta amma rayuwa babu dadi. Ta fara koyon sana'ar dinki amma an koreta saboda ma'aikatan sun ce fuskarta na da bada tsoro.

A Iseyin, ta hadu da wani dan achaba wanda suka fara soyayya amma tana samun ciki ya gudu ya barta. Bayan ta haifa yaro namiji ne 'yan uwanshi suka zo tare da rada masa suna.

A yayin zantawa da Legit.ng, Rokibat tace tana bukatar miliyan biyu domin a yi mata aikin fuskarta karo na biyu a UCH. Tace bata iya numfashi ta hancinta sai dai ta bakinta.

Ga me son taimakwa rayuwar Rokibat, za a iya tuntubar lambar waya kamar haka: +234 813 896 7139.

Z aa iya tuntubar mu ta info@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel