Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun budewa tsohon gwamnan CBN wuta, sun kashe mutum 3

Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun budewa tsohon gwamnan CBN wuta, sun kashe mutum 3

Wasu yan bindiga sun budewa tsohon gwamnan babban bankin Najeriya kuma dan takaran kujerar gwamnan jihar Anambra, Charles Soludo, wuta.

An kashe jami'an yan sanda uku dake gadinsa.

Wannan hari ya faru ne a garin Isuofa, a karamar hukumar Aguata a jihar Anambra yayinda yaje ganawa da wasu matasa a yankin.

Idanuwan shaida sun bayyanawa Daily Trust cewa Soludo na cikin koshin lafiya, babu abinda ya samesa.

Wasu rahotanni sun bayyanawa cewa yan bindigan sun yi awon gaba da kwamishanan kayakkayin jihar, Emeka Ezenwanne.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, DSP Ikenga Tochukwu, ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun budewa tsohon gwamnan CBN wuta, sun kashe mutum 3
Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun budewa tsohon gwamnan CBN wuta, sun kashe mutum 3
Asali: Original

Asali: Legit.ng

Online view pixel