Jerin jihohin Najeriya goma mafi fama da talauci bisa alkaluman NBS

Jerin jihohin Najeriya goma mafi fama da talauci bisa alkaluman NBS

Najeriya kasa ce mai dimbin arzikin man fetur, ma’adinai da filin noma a jihohinta 36. Amma duk da haka wasu jihohina na fama da talauci.

Talauci ya yi wa wasu jihohin katutu sakamakon rashin shugabannin kwarai, almubazzaranci da dukiya da kuma matsalar tsaro.

A cewar rahoton hukumar lissafin tarayya (NBS), an gano jihohi 10 mafi fama da talauci a Najeriya bisa rashin kayan jin dadi, tattalin arziki, tsaro, shugabanci dsss.

Ga jerin matalauta jihohi 10 dake Najeriya:

1. Jihar Sokoto

Jihar Sokoto ce jihar da aka ayyana matsayin mafi talauci a Najeriya saboda matsayin talaucinta ya kai alkalami 81.2%. Yanayin jihar mai tsanani ya sa masu sanya hannu jari basu shiga cibiyar daular Islamiyya.

2. Jihar Kastina

Jihar Katsina dake Arewa maso yammacin Najeriya na cikin matalautan jihohi saboda babu kamfanoni da yawa da zai samarwa gwamnatin jihar kudin shiga mai yawa.

3. Jihar Adamawa

Jihar Adamawa ce jiha aka ayyana matsayin mafi talauci ta uku a Najeriya saboda matsayin talaucinta ya kai alkalami 74.2%.

4. Jihar Gombe

Jihar Gombe ta shiga jerin jihohi mafi talauci a Najeriya saboda matsayin talaucinta ya kai alkalami 73.2%.

5. Jihar Jigawa

Jihar Jigawa na fama da matsalar yara maras zuwa makaranta kuma alkaluman bincike ya nuna talaucinta ya kai 72.1%.

6. Jihar Plateau

Duk da cewa jihar Plateau na cikin jihohi mafi yawan jama’a a Najeriya. Ta yi fama da matsalar rikice-rikicen addini wanda ya lalata tattalin arzikinta da 71%.

7. Jihar Ebonyi

Jiha daya tilo daga kudancin Najeriya da ta samu shiga cikin jerin jihohi mafi talauci ce jihar Ebonyi. Alkaluma sun nuna talaucinta ya kai 70.6% sakamakon rashin shugabancin kwarai da ilimi.

8. Jihar Bauchi

A cewar NBS, Bauchi ta shiga jerin jihohi mafi talauci a Najeriya.

9. Jihar Kebbi

Jihar Kebbi a arewa maso yamma ta shiga jerin jihohi mafi fama da talauci. Alkalumanta 72%.

10. Jihar Zamfara

Da alkaluman talauci 70.8%, NBS ta lissafi jihar Zamfara cikin jerin jihohi mafi talauci a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel