An damke tsohon shugaban JAMB kan bada kwangilan bogin sayan fensira da kilina a kudi N900m

An damke tsohon shugaban JAMB kan bada kwangilan bogin sayan fensira da kilina a kudi N900m

Hukumar yaki da rashawa da laifuka (ICPC) ta sanar da damke tsohon shugaban hukumar shirya jarabawar shiga jami'a watau JAMB, Dibu Ojerinde, kan zargin badakalar milyan 900.

A jawabin da Kakakin hukumar ICPC, Azuka Ogugua ya saki ranar Laraba, an damke tsohon shugaban JAMB din ne ranar Litinin, 15 ga Maris, 2021 a Abuja, rahoton Channels

Ana zarginsa da aikata badakala iri-iri lokacin da yake jagorantar JAMB da NECO.

"Hukumar ta garkame shi don yi masa tambayoyi kan badakalar kudi, kin biyan haraj, zamba cikin aminci, da karerayi," cewar jawabin.

"Hakazalika hukumar na binciken tsohon shugaban JAMB sin kan laifin bada kwangilan boge ga kamfanoni da aka kasa gane inda suka."

An zargi Ojerinda da bada kwangilan sayan fensira da kilina a kudi N900m ga kamfanin Double 07 Concept Limited da Pristine Global Concept Limited, tsakanin shekarar 2013 da 2014.

"Babu hujjan da ya nuna an kawo wadannan abubuwa kuma an kasa gano ya kwangilan," jawabin ya kara.

Yanzu haka an tsare Ojerinde kuma za'a gurfanar da shi a kotu bayan kammala bincike.

An damke tsohon shugaban JAMB kan bada kwangilan bogin sayan fensira da kilina a kudi N900m
An damke tsohon shugaban JAMB kan bada kwangilan bogin sayan fensira da kilina a kudi N900m
Source: UGC

Source: Legit.ng

Online view pixel