Yanzu-yanzu: Dalibai 7 cikin 317 da aka sace sun samu kubuta daga hannun yan bindiga

Yanzu-yanzu: Dalibai 7 cikin 317 da aka sace sun samu kubuta daga hannun yan bindiga

- Labari mai dadi daga garin Jangebe, karamar hukumar Talata Mafara a Zamfara

- Rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikin daliban da aka sace a garin sun dawo gida

Dalibai bakwai cikin yara mata 317 da aka dauke daga makarantar sakandaren GGSS Jangebe a jihar Zamfara sun samu kubuta daga hannun yan bindiga.

Wata majiya ta bayyana cewa daliban sun dawo gida da kansu bayan sun samu ikon sullubewa yan bindigan a cikin daji.

Sun kara da cewa tun daga cikin dajin suka taka sayyada har suka gano gida.

A cewar majiyar, daliban sun bayyana cewa akwai saura dake hanyar dawowa wadanda suka samu kubucewa.

DUBA NAN: Hotunan daliban Karaga bayan sun kwashe kwanaki 9 hannun yan bindiga

Yanzu-yanzu: Dalibai 7 cikin 317 da aka sace sun samu kubuta daga hannun yan bindiga
Yanzu-yanzu: Dalibai 7 cikin 317 da aka sace sun samu kubuta daga hannun yan bindiga
Asali: Twitter

KU KARANTA: Ku daina baiwa yan bindiga kudi ya na da hadari, Buhari ya gargadi gwamnoni

Domin samun nasaran ceto dalibai mata 317 da aka sace ranar Juma'a, gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya nemi taimakon tubabbun dan bindiga Auwalu Daudawa da Zakoa Buhari, ThisDay ta ruwaito.

Auwalu Daudawa ne dan bindigan da ya jagoranci satan daliban makarantan sakandaren GCSS, Kankara, a jihar Katsina. Zakoa Buhari kuma shine dan shahrarren kasurgumin dan bindiga, Buhari Daji.

An sace dalibai a makarantar sakandaren kwana na mata GSSS Jangebe, karamar hukumar Talata Mafara, a jihar Zamfara.

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Asali: Legit.ng

Online view pixel