Da duminsa: Hankalin jama'ar Maiduguri ya tashi sakamakon tashe-tashen Bam da ake ji da yamman nan

Da duminsa: Hankalin jama'ar Maiduguri ya tashi sakamakon tashe-tashen Bam da ake ji da yamman nan

Hankalin mutane a Maiduguri, birnin jihar Borno, ya tashi sakamakon karan tashin bama-bamai da suke ji da yammacin Talata, 23 ga watan Febrairu, 2021.

Har yanzu ba'a fahimci abinda ke faruwa ba, amma mazaunan sun bayyana cewa tun karfe 6 na yamma suka fara jin kararrakin.

TheCable ta bayyana cewa ta samu tattaunawa da wasu mazauna garin inda suka laburta abinda suka gani.

"Ina hanyar zuwa Masallaci na fara jin karan tashin Bam, sannan na fara jin harbe-harbe, " daya daga cikin mazaunan yace.

"Karan na zuwa daga yankin Gwange," ya kara.

Wani mazaunin a cewar TheCable ya bayyana cewa ana kyautata zaton yan Boko Haram ne suka kai hari.

"Labarin da na samu shine yan ta'adda na kokarin shigowa gari ta kauyen Meri, kusa da jami'ar Maiduguri," yace.

Da duminsa: Hankalin jama'ar Maiduguri ya tashi sakamakon tashe-tashen Bam da ake ji da yamman nan
Da duminsa: Hankalin jama'ar Maiduguri ya tashi sakamakon tashe-tashen Bam da ake ji da yamman nan
Source: Original

Source: Legit.ng

Online view pixel