Masu garkuwa da mutane sun bawa mutanen da suka kama N10k su sayi takalmi bayan karbar kudin fansa

Masu garkuwa da mutane sun bawa mutanen da suka kama N10k su sayi takalmi bayan karbar kudin fansa

- Wasu masu garkuwa da mutane sun rabawa mutanen da suka kama kam N60,000 domin sayen takalma

- 'Yan ta'addar sun bayar da kyautar naira dubu goma ga kowanne daya daga cikin mutanen shida suka sace

- Wata majiya ta sanar da manema labarai cewa dangi da 'yan uwan mutanen da aka sace sun hada N1.7m a matsayin kudin fansa

Rahotanni sun bayyana cewa masu garkuwa da mutane sun rabawa wasu mutane da suka yi garkuwa da su kyautar N10,000 duk mutum guda, domin sayen takalma, a lokacin da suka sake su.

Mutane shida ne rahotanni suka bayyana cewa an yi garkuwa da su a ranar Alhamis, inda aka shigar da su dajin jihar Kogi ba tare da takalma a ƙafafunsu ba, kamar yadda Insidearewa ta wallafa.

An ruwaito cewa, kwanaki 5 bayan faruwar lamarin, yan uwan wadanda aka yi garkuwa da su, da ke zaune a garin Avu a karamar hukumar Abugi, jihar Niger, sun hada Naira miliyan daya da dubu ɗari bakwai, inda suka biya kudin fansar mutanen kamar yadda masu garkuwan suka bukata.

Daga cikin wadannan kudaden ne yan bindigar suka rabawa mutanen 6 dubu sittin domin sayan takalma.

Masu garkuwa da mutane sun bawa mutanen da suka kama N10k su sayi takalmi bayan karbar kudin fansa
Masu garkuwa da mutane sun bawa mutanen da suka kama N10k su sayi takalmi bayan karbar kudin fansa
Asali: Facebook

Daya daga cikin mutanen da suka kuɓuta, da ake kira Abdulsalami, ya labarta cewa yan bindigar bayan karbar N1.7m, sun raka su nesa kadan da garinsu inda suka sake su da misalin ƙarfe 1 na dare.

Abdulsalami, ya shaidawa yan uwansu halin da suka kasance ciki a hannun masu garkuwa da mutanen, yana mai cewa, sun yi tafiya a kasa ta tsawon awanni, kafin suka isa nahiyar yan ta'addan da ke cikin dajin Jihar Kogi.

Wani shugaban garin, Musa Idris, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa sai da aka biya kudin fansa kafin karbo mutanen.

A ranar Lahadi ne Legit.ng ta rawaito cewa Obasanjo ya yi Allah ya isa yayin da ya ke bayyana cewa yana da masaniyar cewa marigayi Umaru Musa Yar'adua bashi da koshin lafiya kafin ya goyi bayansa.

Tsohon shugaban kasar ya musanta zargin cewa kutunguila da kitimurmura suka sanya shi bawa Yar'adua takara a 2007.

Obasanjo ya jingine manyan 'yan siyasa da suka hada da tsohon shugaban kasa, Ibrahim Babangida, da mataimakinsa a wancan lokacin, Atiku Abubakar, tare da goyawa Yar'adua baya wajen samun tikitin takara a jam'iyyar PDP.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel