Da duminsa: Dambe ya rincabe a majalisar dattawa, wasu suna gudun ceton rai

Da duminsa: Dambe ya rincabe a majalisar dattawa, wasu suna gudun ceton rai

- Wasu 'yan majalisa sun bai wa hammata iska yayin wani zama na majalisar tarayya

- Wadanda suka kwashi damben 'yan majalisar ne na yankunan da ake samun man fetur

- Take a wurin aka ga wasu daga cikin 'yan majalisun suna tserewa don neman tsira

Dambe ya barke yayin da wasu 'yan majalisa na bangaren da ake samun mai suka je gabatar da wata muhimmiyar bukatarsu ga majalisa.

Vanguard bata riga ta tabbatar da sunayen 'yan majalisar ba, amma tabbas masu wakiltar bangarorin da ake samun man fetur ne.

Fadan ya barke ne da misalin karfe 12:10pm yayin da shugaban kwamitin rikon kwarya na PIB, Hon. Mohammed Monguno ya gayyaci 'yan majalisar don su gabatar da bukatunsu.

Har yanzu 'yan majalisar suna ta ranta a na kare don gudun jikinsu yayi tsami sakamakon mugun damben da ake yi.

KU KARANTA: Dan Najeriya ya gina katafaren gida da robobin lemu da ruwa cike da kasa (Hotuna)

Da duminsa: Dambe ya rincabe a majalisar dattawa, wasu suna gudun ceton rai
Da duminsa: Dambe ya rincabe a majalisar dattawa, wasu suna gudun ceton rai. Hoto daga @NGRSenate
Source: Twitter

KU KARANTA: COVID-19: Ba za mu tirsasawa jama'a yin riga-kafi ba, Sarkin Musulmi

A wani labari na daban, kungiyoyin 'yan bindiga biyu sun yi arangama a kauyen Illela da ke karamar hukumar Safana ta jihar Katsina, lamarin da ya kawo halakar 'yan bindiga masu yawa sannan wasu suka samu miyagun raunika.

Rikicin ya barke tsakanin sansanin Mani Sarki da Dankarami da ke sansaniin Abu Rada a ranar Alhamis da ta gabata.

Majiyoyi sun sanar da Daily Trust cewa, Sarki wanda yanzu tubabben dan bindiga ne wanda ya mora rangwamen gwamnati ana kallon shi a matsayin bare a sauran sansani da ke dajikan.

An gano cewa sasancin da Sarki yayi da gwamnati ne yasa ya koma kauyen Illela domin fara sabuwar rayuwa amma wasu daga cikin yaransa suka ki biyayya gare shi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel