Arangamar kungiyoyin 'yan bindiga biyu ya kawo salwantar rayukan 'yan ta'adda masu yawa a Katsina

Arangamar kungiyoyin 'yan bindiga biyu ya kawo salwantar rayukan 'yan ta'adda masu yawa a Katsina

- Kungiyoyin 'yan bindiga biyu masu kishi da juna sun yi mummunan arangama a Katsina

- An gano cewa wani dan bindiga ya sace matar daya kuma sai da ya karba N500,000 sannan ya sakota

- Hakazalika, wata kungiyar ta kai hari Illela amma wata kungiyar ta hana ta aiki har ta kwace musu makamai

Kungiyoyin 'yan bindiga biyu sun yi arangama a kauyen Illela da ke karamar hukumar Safana ta jihar Katsina, lamarin da ya kawo halakar 'yan bindiga masu yawa sannan wasu suka samu miyagun raunika.

Rikicin ya barke tsakanin sansanin Mani Sarki da Dankarami da ke sansaniin Abu Rada a ranar Alhamis da ta gabata.

Majiyoyi sun sanar da Daily Trust cewa, Sarki wanda yanzu tubabben dan bindiga ne wanda ya mora rangwamen gwamnati ana kallon shi a matsayin bare a sauran sansani da ke dajikan.

KU KARANTA: Biyu daga cikin yara 18 da aka dawo dasu daga Anambra 'yan jihar Kano ne

Arangamar kungiyoyin 'yan bindiga biyu ya kawo salwantar rayukan 'yan ta'adda masu yawa a Katsina
Arangamar kungiyoyin 'yan bindiga biyu ya kawo salwantar rayukan 'yan ta'adda masu yawa a Katsina. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

An gano cewa sasancin da Sarki yayi da gwamnati ne yasa ya koma kauyen Illela domin fara sabuwar rayuwa amma wasu daga cikin yaransa suka ki bin shi.

Wata majiya tace: "Wasu 'yan bindiga da suka samu jagorancin Dan Da daga sansanin Alhaji Dankarami sun kai hari yankin Illela amma aka taru aka koresu.

"Hakan ne yasa suka tsere tare da barin makamansu wanda suka hada da bindigar harbo jirgin sama. Hakan ya mutukar fusata 'yan bindigan kuma yasa suka dauka alwashin daukar fansa.

"Na biyu kuwa, kanin Sarki Mani ya taba sace matar daya daga cikin 'yan bindigan bangaren Dangwate kuma har sai da aka biya N500,000 sannan ya saketa."

Majiyoyi sun tabbatar da cewa an kashe kanin Sarki da ake kira da Chirwa tare da matarsa yayin da wasu suka samu miyagun raunika.

KU KARANTA: Jerin sunaye: Shugabannin dakarun sojin kasa na Najeriya tun daga 1999 da jihohinsu

A wani labarina daban, NGF ta ce ba canza shugabannin tsaro ne kadai zai kawo garanbawul ba ga matsalolin tsaron da Najeriya take fuskanta, Punch ta wallafa hakan.

Wajibi ne shugaba Muhammadu Buhari ya sanya ido kuma ya dinga bai wa shugabannin tsaro umarni yadda ya dace a matsayinsa na kwamandansu.

"Babban matakin da Buhari zai dauka shine canja salo da kuma fuskantar matsalolin tsaro gadan-gadan. Sai ka ji yana cewa ya taras da tabarbarewar tsaron Najeriya a 2015 ya nunka halin da ake ciki yanzu, wannan kalaman suna matukar tayar da hankali."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel