COVID-19: Ba za mu tirsasawa jama'a yin riga-kafi ba, Sarkin Musulmi

COVID-19: Ba za mu tirsasawa jama'a yin riga-kafi ba, Sarkin Musulmi

- Sarkin musulmi na Sokoto, Alh. Muhammad Sa'ad Abubakar III ya shawarci gwamnati da kada ta takura wa jama'a akan riga-kafin cutar COVID-19

- A cewarsa, matukar ana son a samu nasara, wajibi ne malaman addini da shugabannin gargajiya su hada kai wurin wayar wa jama'a kai akan ta

- Ya kara da cewa, jama'a da dama za su kirkiro labaran bogi da karairayi akan riga-kafin, ta hanyar wayar da jama'a kawuna ne kadai za a samu nasara

Sarkin Musulmi na Sokoto, Alh. Muhammad Sa'ad Abubakar III, a ranar Laraba ya shawarci gwamnati da kada ta matsa wa 'yan Najeriya akan riga kafin COVID-19.

Ya bayar da wannan shawarar ne yayin da yake jawabi a wani taro na limamai da malaman addini akan COVID-19 wanda aka yi a Abuja, Vanguard ta wallafa.

Sarkin ya bayar da shawarar kada a takura wa 'yan Najeriya don su amince da riga-kafin, amma a dinga ilimantar da su da kuma basu bayanai masu kyau akan cutar.

KU KARANTA: Marasa rinjayen majalisar dattawa sun mika bukata 1 ga sabbin hafsoshin tsaro

COVID-19: Ba za mu tirsasa jama'a yin riga-kafi ba, Sarkin Musulmi
COVID-19: Ba za mu tirsasa jama'a yin riga-kafi ba, Sarkin Musulmi. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

Kamar yadda yace: "Ya kamata a dinga zama ana tattaunawa da mutane don a fahimtar dasu amfanin yin allurar ga lafiyarsu, daga nan za su amince. Ba wai a takura musu ba.

"Lokacin da Allah ya kai ni wannan matsayin a 2006, ana tsaka da neman yadda za a yi riga-kafin cutar polio.

"A lokacin, ministan lafiya, Farfesa Babatunde Osotimehin ya tunkareni da maganar don mu fahimtar da mutane. Anan na amince saboda muna son mu ga mutane cikin koshin lafiya."

"Haka muka samu shugabannin gargajiya daga jihohin arewa 19 da Abuja, a haka muka shirya kwamitin shugabannin gargajiya na polio. Kuma kwamitin ya yi aiki kwarai, yanzu haka shekaru 13 kenan da aka magance cutar.

"Wannan yana daya daga cikin amfanin shugabannin gargajiya. Amma shugabannin gargajiya ba za su iya yin irin wannan wayar da kan ba kamar shugabannin addini.

"Duk wani basarake da baya da kusanci da malaman addini ba mutumin kwarai bane. Sakamakon hadin kai da malaman addini ne ya janyo nasarar kawar da cutar polio." Yace.

A cewarsa, za a wallafa labaran kanzon kurege akan riga kafin COVID-19, sakamakon karancin ilimi akanta, don haka wajibi ne a wayar da kan jama'a.

KU KARANTA: Dalilin da yasa Buhari ya sallami hafsoshin tsaro, Fadar shugaban kasa

A wani labari na daban, a ranar Talata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya maye gurbin hafsoshin tsaron kasar nan da suka kasance a ofishinsu tun 2015 da wasu sabbin, The Cable ta wallafa.

Kafin daukar wannan matakin, jama'a da dama sun dinga kira ga shugaban kasar da ya sallami hafsoshin tsaron sakamakon hauhawar rashin tsaro a fadin kasar nan.

A yayin da shugaban kasan ya nada sabbin hafsoshin tsaron, 'yan Najeriya sun dinga bayyana ra'ayoyinsu a Twitter da yadda suke ji game da wannan cigaban.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel