Shugaba Buhari ya sake alawus na ASUU har Naira biliyan 40

Shugaba Buhari ya sake alawus na ASUU har Naira biliyan 40

- Gwamnatin tarayya ta biya Naira biliyan 40 na kudaden alawus din kungiyar ASUU

- Ministan kwadago ya bayyana yafiyar da shugaban kasa ya yiwa ASUU na batun 'ba aiki, ba albashi'

- Gwamnati ta kuma bayyana akwai yiwuwar sake wasu Naira biliyan 30 a karshen watan Janairun 2021

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi watsi da dokar ‘babu aiki, babu albashi’ da ya jawo yajin aiki ga malaman jami’o’i don ba da damar zaman lafiya da ci gaba, in ji Ministan kwadago da samar da ayyuka Dr. Chris Ngige, a karshen mako.

Gwamnati ta saki Naira biliyan 40 domin biyan alawus din malaman jami’o’i da alawus alawus na ma’aikatan da ba sa fannin karantarwa, The Nation ta ruwaito.

KU KARANTA: Masu kiwon kaji na rokon Buhari kan shigo da masara da waken soya daga kasar waje

Shugaba Buhari ya sake alawus na ASUU har Naira biliyan 40
Shugaba Buhari ya sake alawus na ASUU har Naira biliyan 40 Hoto: PM News
Asali: UGC

Hakanan, gwamnati zata saki zunzurutun kudade Naira biliyan 30 zuwa karshen wannan watan ga jami'o'in don farfado da ma'aikatan jami'o'i.

Daga cikin Naira biliyan 40, kimanin Naira biliyan 10 ne aka ware don biyan alawus alawus na mambobin Kungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’o’in Najeriya (SANU), da Kungiyar Ma’aikatan Jami’a (NASU) da masana fasaha.

Ngige ya ce: “A zahiri, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi wa mambobin ASUU rangwamen/yafiya akan ba aiki, babu biyan albashi a cikin dokar Rigingimun Ciniki na kasar.

Game da kudaden farfadowa Naira biliyan 30 da ASUU ta nema, Ngige ya ce: "zuwa karshen watan Janairu, gwamnati za ta biya."

KU KARANTA: ‘Yan Bindiga sun sace marayu 8 da wasu 3 a gidan marayu na Abuja

A wani labarin, Masu cin gajiyar N-Power, wadanda suka kammala shirin aikin na shekaru biyu, yanzu za su sami damar samun aikin dindindin ko damar kasuwanci, in ji Gwamnatin Tarayya.

Wannan wani bangare ne na sabuwar kokarin gwamnati kan fita daga tsarin N-power.

Tsarin an yi shine ga dukkan 'yan tsarin A da B na shirin N-Power.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel