Kwanaki 9 a jere, kullum sai mutane sama da 1000 sun kamu da Korona

Kwanaki 9 a jere, kullum sai mutane sama da 1000 sun kamu da Korona

- Adadin masu kamuwa da Korona yana karuwa kullum tun da aka shiga sabuwar shekara

- Kwanaki 9 a jere, yan Najeriya sama da 1000 ke kamuwa da Korona

- Gwamnatin tarayya ta yi barazanar sake kafa dokar hana fita idan adadin ya cigaba da karuwa

Mutane 1270 kwayar cutar ta harba a fadin Nigeria a ranar Talata, 13 ga watan Junairu 2021, kamar yadda alkaluman hukumar hana yaduwar cututtuka NCDC ta saba fitarwa kullum.

Adadin da aka samu ranar Alhamis ya kai jimillan wadanda suka kamu da cutar 102,601 a Najeriya.

Daga cikin mutanen da suka kamu, an sallami 81,574 yayinda 1373 suka rigamu gidan gaskiya.

Cikin kwanaki tara da suka gabata, kulli yaumin sai an samu akalla sabbin masu kamuwa 1000.

Kalli jerin addadin wadanda suka kamu tun ranar 4 ga Junairu zuwa 12 ga wata:

4 ga Junairu - Mutane 1204

5 ga Junairu - Mutane 1354

6 ga Junairu - Mutane 1664

7 ga Junairu - Mutane 1565

8 ga Junairu - Mutane 1544

9 ga Junairu - Mutane 1585

10 ga Junairu - Mutane 1024

11 ga Junairu - Mutane 1244

12 ga Junairu - Mutane 1270

Kwanaki 10 a jere, kullum sai mutane sama da 1000 sun kamu da Korona
Kwanaki 10 a jere, kullum sai mutane sama da 1000 sun kamu da Korona Source: Presidency
Source: Facebook

Source: Legit

Online view pixel