Ra’ayi: POS: Tarihinsa da hukuncin amfani da shi, Daga Farfesa Ahmad Murtala

Ra’ayi: POS: Tarihinsa da hukuncin amfani da shi, Daga Farfesa Ahmad Murtala

POS: TARIHINSA DA HUKUNCIN AMFANI DA SHI WAJEN KASUWANCI DA FITAR DA KUDADE DA TURASU

Prof Ahmad Murtala.

Bismillahir Rahmanir Rahim

Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga Annanbinmu Muhammad da Iyalensa da Sahabbansa bakidaya.

Bayan haka, a yau Laraba 23 Jumada Ula, 1442 H.-06 Janairu, 2021 M., na sami tambaya ta fuskoki da yawa har sai da aka rubuto cewa: “Malam ana cikin bukatuwar yin cikakken bayani a dangane da POS. Wasu malaman sun haramta, wasu kuma sun halatta, Mun gode”. Wannan ita ce tambayar.

Amma jin akwai wannan sabani na malamai a nan Kasar, ya sa na yi kamar ba zan bada amsa ba. Saboda ban cika son shiga irin mas’alolin da aka sami kare kaina ba, ba tare da na ji ko na karanta abin da kowane bangare ya fada ba.

Sai dai tambayar ta zo daga wajen wani mutum mai kima a idona. Don haka na rubuta wannan bayani. Amma ba wai na rubuta ba ne a matsayin dole sai na gamsar da kowa da kowa ba. Wannan ba zai taba yiwuwa ba.

Ra’ayi: POS: Tarihinsa da hukuncin amfani da shi, Daga Farfesa Ahmad Murtala
Ra’ayi: POS: Tarihinsa da hukuncin amfani da shi, Daga Farfesa Ahmad Murtala Hoto: Nairametrics
Asali: UGC

Na dubi mas’alar ne da kyau gwargwadon abin da Allah ya huwace a yanzu-yanzu. Allah ya bamu sa’a da dacewa.

1-Yana da kyau a rika sanin tarihin wasu abubuwa da yadda suka taso da yadda suke amfani da sauran wasu abubuwan da suka shafesu. Saboda ta haka ne za a iya basu hukuncin da ya dace da su a Shar’ance.

Imamu Shafi’i yana cewa, “Na dauki lokaci ina karanta ilimin tarihi, shekara kaza da kaza! Amma na karantashi ne kurum don na taimaka da shi wajen fahimtar ilimin Fikihu”.-(Al-Istiksa Li Akhabril Duwalil Magribil Aksa:1/59)

الإمام الشافعي رضي الله عنه كان يقول:"دأبت في قراءة علم التاريخ كذا وكذا سنة وما قرأته إلا لأستعين به على الفقه".

2-Akan haka, bari mu fara da dan tarihi kadan. Abin da ake nufi da PoS shi ne ‘Point of Sale’ "نقاط البيع" .

A wani lokacin kuma ana kiransa da sunan POP wato Point of Purchase. Duka biyun a asalinsa suna nufin tsarin kididdige cinikin da mai kanti ya yi a nan take ba tare da wata wahala ba. An fara kirkiro tsarin POS tun a 1879 M. Da sunan ‘Cash Register’.

Sunan wanda ya fara kirkiroshi James Ritty. Yana da babban shago kayan masarufi. Amma sai ya fahimci ma’aikatansa suna yi masa dingushe.

Don haka sai ya sa aka kirkiro inji da sunan ‘Incorruptible Cashier’ don ya rika sanin adadin abin da ya shigo lalitarsa.

A 1906 a ka fara jona wannan inji da wuta, ta yadda ya kara sauri wajen aikinsa. Sai kuma a shekarun 1970s aka fara hada wannan fasaha da na’ura mai kwakwalwa. Haka ya wanzu har shekarun 1990s a inda aka fara kera injina na zamani, wadanda su da kansa kwanfiyuta ne.

Shegowar shekarun 2000s a nan ne aka fara samar da irin wadannan injin amma wadanda za a iya dauka a hannu daga nan a kaisu can, suna kiransu da ‘mPOS’-wato Mobile POS.

3-Tsarin POS ya shigo Nigeria sosai 2012 M. A lokacin da Babban Bankin Tarayya ya huwacewa ‘yan kasa su rika amfani da shi saboda rage zirga-zirga da kudade a hannu. Kafin haka kaso 90% na cinikayya ana yinsu da kudade a hannu tsirara! –(Challenges to the Efficient Use of Point of Sale (POS) Terminals in Nigeria na Adeoti).

4-Akwai POS kala-kala wanda kamfanoni da wuraren sayar da abinci da abin-sha da otel-otel suke amfani da su.

Kowanne yana neman wanda ya dace da bukatarsa. Amma amfani da POS a matsayin wurin da za a iya zuwa a nemi su baka wani gwargwado na kudi, su kuma su yi amfani da katin mutum na ATM su dibi wannan kudin su tura zuwa account dinsu a maimakon wanda suka bashi a nan take, wannan ya fara ne a ‘yan shekarun nan, ba da dadewa ba.

5-Kafin mutum ya bude wurin harkar POS sai ya bi wasu matakai kamar haka:

i- A dokokin Kasa an yarda a bude irin wadannan wurare kamar yadda aka fada a baya.

ii- Masu harkar POS suna da alaka da bankuna ta fuskar sai sun je sun yi rijista da wani banki tukuna. Daga cikin hikimomin yin haka shi ne don bankin zai ga ana hadahadar kudade masu yawa akai-akai, sai ya zamo ba zai damu ba, saboda ya yarda da account din da ake wannan hadahadar da shi.

iii- Akwai certificate da bankin zai bawa wanda ya yi rijista da shi a matsayinsa na “agent”-wakilinsu. Don haka zai yi rawa da bazar wannan bankin a iya bangaren da suka yarjewa POS ya yi hidima.

iv- Bankin da aka yi rijista da shi yana son ya ga motsin wannan POS a kalla sau goma a rana don ya tabbatar da yana aiki. Wannan ba tare da ya kula da yawan kudin da zasu shiga ko zasu fita ba ta hanyar wannan POS din.

v-Zai biya kudin hayar shago da wutar lantarki da kudin data da yake amfani da ita don hawa kan intanet ko kudin cajin waya, da sauransu.

6-Mafi girman ayyukan da masu shagunan POS suke yi guda biyu ne:

a- Zasu bada kudi cash ga wanda yake so, sai su karbi ATM card dinsa su ciri daidai kudinsu su tura cikin account dinsu. Misali an biyashi albashi dubu goma (10,000) sai ya zo suka bashi tsurar kudi dubu goma cash, sannan sai ya basu katinsa mai dauke da wadannan kudade, sai su kwashe daidai kudin da suka bashi daga accout dinsa zuwa nasu.

b- Mutum zai iya kawo kudi kamar dubu goma ya ce a tura masa cikin account dinsa ko kuma a turawa dansa da yake karatu a wata kasa ko a tura a account na mahifiyarsa ko dan uwansa ko zai biya kudin wutar lantarki, ko kudin makaranta, da dai sauransu.

A duk wadannan hidimomi da masu shagon POS suka yi, zasu bukaci a basu wani abu a matsayin ladan aikin da suka yi. A yadda al’adarsu ta gudana a yanzu akwai wani gwargwado na kudi mara yawa da suke karba bisa duk dubu daya ko biyar ko goma ko dari ko miliyan daya da suka bawa mutum ko suka tura masa.

Za a iya basu daga account din mutumin idan da akwai wasu kudin a ciki ko ya kawo ladan ya basu hannu-da-hannu daga cikin kudin da suka bashi.

7-Wadannan ayyuka na POS dukansu sun halatta ta fuskoki marasa iyaka ba tare da wani dabaibayi ba.

Ga kadan daga cikinsu:

i- Akwai abubuwa masu yawa da banki koda kuwa wanda ba na Musulunci ba ne yake yi. Kuma ba a kirgasu a matsayin haram. Wannan sun hada da tura kudi daga wani wuri zuwa wani “transfer” "التحويلات المصرفية. Wannan ba wani laifi a kansa.

Mutum kuma zai biya banki ladan aikin da ya yi masa. Abin da masu shagunan POS suke yi a matsayinsu na wakilan banki, wadanda ya san da zamansu a wannan sana’a, bai gaza ko kuma na ce irinsa ne kwabo-da-kwabo da wanda bankunan suke yi.

Malaman zamani kuma bakidaya suka ce daidai nan yana da kyau a aikin banki. Wato ba haram ba ne a biya banki kudin aikin transfer-(Kararu Majma’ul Fikihil Islami:9/1/370; Al-Bunukul Islamiyya na Abdullahi Addayar sh/25; Al-Ma'amalatul Masrafiyya Wa Hukmuha Fil Islam sh/14-15; Al-Masariful Islamiyyah: Dirasah Li Adadin Minha na Rafik Yunus Al-Misri, sh/53-55; Al-Mu’amalat Al-Maliyyah Fil Fikihil Islami Asalah Wa Mu’asarah na Debian bn Muhammad:12/234-243)

ii- A zahiri ma shagon POS wani karamin banki ne da yake gudanar da wasu daga ayyukan bankin da yake da rijista da su. A lokacin da mutum ya yi amfani da ATM ya debo kudi daga injin da banki suka ajiye don dibar kudade, zai ga bankin sun debi wasu ‘yan kudade na hidamar da suka yiwa mutum.

Bankin da mutum yake da account suna dan yi masa ragi. Amma wani bankin daban suna diba fiye da yadda nasan suka diba. Don haka, shi kansa mai POS ba dalilin da zai sa ba zai karbi wani kaso na hidamarsa ba!

iii- Masu POS cikakkun wakilai ne na karbar kudin mutum daga bankinsa zuwa nasu, sannan sai su bashi daga kudinsu. Saboda wakilce taimako ne kamar yadda Ibnul Arabi Al-Maliki yake fada "الوكالة معونة".- (Ahkamul Kur’ani: 3/223).

Malamai sun bayyana cewa ba laifi ka sa wakili sannan ka biyashi ko kuma in ya ga dama ya yi maka wakilcin Fisabilillahi, ba tare da an biya shi komai ba. Imamu Ibnu Kudama ya na cewa: “Ya halatta a yi wakilci ko don wani abu da za a bayar ko kuma ba tare da shi ba”-(Al-Mugni na Ibnu Kudama: 5/95) قال الإمام ابن قدامة:"يجوز التوكيل بجُعُل، وبغير جُعُل"

A zamanin yanzu ba dole ba ne sai an tura wani ya je bankin da kafa sannan za a ce an yi wakilci. Hatta tura kudin zuwa account din mai POS a matsayin kamar an je an karbo yake, irin abin da malamai suke kira da “Karbar abu a Ma’ana” "القبض الحكمي".

Tunda kudin sun shiga lalitarsa, ba laifi don ya bayar da su ta kowace irin fuska.Wato ko ya dauko wannan da ya turawa kansa ya bawa mai kudin ko kuma ya bashi wasu da yake da su. Sannan a bashi ladansa.

iv- Masu POS suna yin amfani da kwarewarsu da wani bangare na kudin da suka sa a katin wayarsu ko na data din da suka saya. Haka nan suna amfani da wutar lantarki da injin POS din kansa da suka saya da zaman da suke yi na kudi a shaguna.

Bugu da kari, sun ragewa mutane wahalar bin layin ATM ko na cikin bankuna da aka saba yi. Wannan duka a bayyane yake cewa sun yi wa mutum aiki, don haka masu POS suna da cikakken hakkin a biyasu kudin wahalarsa.

v- Kowace mu’amalla tana da asali guda biyu; “Halasci” da “Inganci” الإباحة والصحة. Babu wani dalili da zai haramta sana’ar POS. Sannan kuma masu yinta a halin yanzu suna gudanar da ita bisa asalin inganci. Don haka ba haram suke ci ba, ba kuma batacciyar sana’a suke gudanarwa ba.

vi- Ba bu wani abu na haram ko riba a cikin mu’amalla guda biyu da ake gudanarwa ta hanyar POS. Domin riba tana shiga abubuwa guda uku ne kurum, kuma ba bu wata hanya da zasu shiga wannan mu’amalla:

a-Ciniki: Ba wata cinikayya aka kulla tsakanin mai POS da wanda ya zo masa don ya fito masa da kudi ko don ya tura masa ba. Don haka riba ba zata shiga wannan bangaren ba.

b-Bashi: Ba wani bashi a cikin wannan mu’amalla ta POS. Domin da ya zo shagon POS cewa ya yi yana da kudi (10,000) a cikin wannan ATM din a kwashesu a tura wani account din amma a bashi kudin cash.

Wannan ‘transfer’ kenan ba bashi ba ce. Don haka riba ba zata shiga ba. Kada a dauka don ya zo ya bawa mai POS katin ATM dinsa, shi kuma ya tura kudi zuwa nasa account din cewa bashi ya bashi. Kudin kuma da zai ba shi hannu-da-hannu biyan bashin ne. Wannan ba haka ba ne. Domin ‘An daukar komai da manufarsa’ "الأمور بمقاصدها" kamar yadda wata Ka’ida ta fada.

An gina mu’amallar ne a kan ‘transfer’, wadda daman bankuna suna yinta. Mai POS ya debo kudin daga wani account ne ya zuba a account dinsa, sannan ya bada su cash.

Ko da za a ce banki su ma ajiya, ake cewa mutum, ya kai musu, amma kuma aka hana mu'amallar, saboda ta ginu ne a kan bashi. Wannan haka yake ta fuskar cewa su banki tun ranar da aka kafa tsarin bankunan da aka saba da su yau-da- gobe (Conventional Banks) ya ginu ne a kan bashi da ruwa.

Sañnan har yanzu haka yake a rubuce a kan dokokinsu. Ko da mutane suna cewa sun kai ajiyar kudade banki, shi banking ya san ba ajiye aka kai masa ba, shi a wurinsa rance aka ba shi. Amma sabanin wañnan mu'amalla ta POS wadda tun asali tsakanin mai kudi a ATM da mai shagon POS ba wanda yake da manufa ta bashi da rance, kowannensu manufarsa ita ce za a yi transfer ta kudi kawai. Don haka suka bambanta da tsarin da mutanen suke kira "ajiya a banki".

Wani abu mai matukar muhimmaci da ya kamata kowa ya dada ganeshi shi ne idan har mun kaddara cewa alakar bashi da rance ce tsakanin mai POS da mai kudi, to abin la'akarin shi ne shi mai kudin shi ne fa ya bada rance sañnan shi ne kuma dai ya bada karin da sunan ladan aiki.

Ba wai mai shagon POS ne ya mayar da kudin da aka ranta masa (in har mun dauka ma bashi aka bashi!), sannan ya kara wani abu ba. Domin malamai sun fada riba ita ce kudin da wanda ya karbi rance zai mayar da kudin da aka bashi da wani kari.

A mas'alar POS kuwa ba shi ne ya kara ba, shi aka karawa. Wañnan yanayin kuwa ba malamin da ya kirawoshi da sunan riba!!

A yi la'akari da wañnan sosai, domin ina ganin rashin ganeshi da fayyace ne ya sa wasu suke daukar akwai riba a mu'amalar POS, wanda kuma a hakika, kamar yadda aka gani, ba bu!

c- Canji: Duk da akwai burbushin cinikayya a cikin canji, sai dai ana wareshi saboda karfin ma’anar da take cikinsa wadda zata iya sawa ya ci gashin-kansa. Abin nufi dai masu POS ba canji suke yi ba. Kudin mutum ne za a bashi irinsu. Sai dai a lokacin da ya bada Naira aka turawa dansa ko wakilinsa a wata kasa, zai debi daidai da canji da kimar wannan kudi a can.

Abin da hadisai suka hana na canji kamar wanda ya shafi dinare da dinare ko azurfa da azurfa ko naira da naira ko dala da dala shi ne, misalin a sami jan gwal sosai da kuma farin gwal, wanda ba mai ja sosai ba, sai a ce za a dauki wani abu a cikin wanda ba mai ja sosai din ba.

Kamar sabuwar naira da tsohuwa, sai a ce za karbi wani abu a wurin mai tsohuwa. Wannan shi ne haram. Amma idan ya zamo gwal ko naira din suna wani account sai aka turashi wani account din daban sannan aka bawa mutum irinsa, shi kuma ya bada ladan wani kudi don wahalar turawa da rage masa wahalar zuwa banki da aka yi, wannan ba lifi.

Shi kuwa mai POS ya bawa mutum kudinsa yadda suke, sai dai ya ce za a bashi kudin fito da ya yi! Ba wai zuwa ya yi a misali ya mika masa 10,000 shi ma ya mika masa 9,990 a matsayin canji ba.

Wannan naira darin ta ladan fito zai iya ba shi ita daban, zai iya kuma cireta daga cikan kudin a matsayin ladan aikinsa. Masu canji kuwa cewa zai yi zan baka sababbin 'yan naira dari-dari na 10,000 amma zaka dora mini naira dari, to a nan sai a ce an yi riba! Domin amfanin sabuwar naira dari da tsohuwa duk daya ne, ba bu dalilin karbar wani abu a nan!

A cikin Mazahabin Hambaliyya, duk da cewa sabanin Mazahabin Jumhurun Malamai ne, amma sun halatta cewa mutumin da ya sana’anta wani gwal ya zubashi a wata kama da ado na musaman a zo a sayi gwal da kudin da ya yi daidai da shi, sannan a kara wani abu a matsayin ladan sana'arsa da fusahar da ya nuna a wajen kera dankunne da sarka da wannan gwal din.

Shehul Islami Ibnu Taimiyya da Ibnul Kayyim da Ibnu Mani’, duk sun tafi a kansa haka. Sheikh Al-Mardawai ya ce, 'A kan haka fatawar malamanmu na Hambaliyya ta gudana'. Ga kuma bayanin da Ibnu Kudama ya yi. Ya ce: “Idan mutum ya ce da gursimeti ka kera mini zobe azurfa, nauyinsa kamar dirhami daya, zan biyaka dirhami dayan. Sannan zan baka wani dirhamin a matsayin ladan aikinka, wannan ba ya cikin irin abin da aka hana sayar da dirhami daya da guda biyu. Malaman Mazahbinmu na Hambaliyya suka kara da cewa: gursimetin zai iya karbar dirhami biyun, daya a matsayin kudin zoben, dayan kuma sakamakon ladansa“-(Al-Mugni na Ibnu Kudama: 4/130-131; Al-Majmu’u na Nawawi:10/87-88; Al-Ikhtiyarat Al-Fikhiyyah na Al-Ba’ali:sh/473; Al-Fatawal Kubra na Ibnu Taimiyyah:5/391, I’lamul Muwakki’in na Ibul Kayyim: 2/159-162, Al-Furu’u na Ibnu Muflih:4/149; Al-Insaf na Ala’uddini Al-Mardawi:5/15; Azzahbu Wa Ba’adu Khasa’isihi Wa Ahkamihi na Ibnu Mani’ a Majallar Majma’ Fikhil Islami, Al-Mu’amalat Al-Maliyyah Fil Fikihil Islami Asalah Wa Mu’asarah na Debian bn Muhammad:11/273-322)

قال الإمام ابن قدامة:"فأما إن قال لصائغ: اصنع لي خاتما؛ وزنه درهم، وأعطيك مثل زنته. وأجرتك درهما. فليس ذلك بيع درهم بدرهمين. وقال أصحابنا للصائغ أخذ الدرهمين؛ أحدهما في مقابلة الخاتم. والباقي أجرة له".

8-Kulawa kada mutum ya fada cikin haram ko ya ci riba yana daga cikin muhimman abubuwan da Musulmi yake kokari a kowane lokaci. Sayyadina Umar ya yi bayanin yadda mas’alolin riba suke da wahalar sha’ani wajen ganesu, sannan ya ce, “Ku kauracewa riba da duk wani abu na kokwanto”.-(Sunanu Ibnu Majah, L:2276)

قال عمر بن الخطاب- رضي الله عنه -"دعو الربا والريبة".

Duk wata mu’amalla da wani yake yi, in ya ji shi a zuciyarsa bai gamsu da ita ba, sai kurum ya kaurace mata. Wannan kuma bai hana wadanda suka gamsu da ita su ci gaba da yinta ba, matukar akwai mafita ta Shari’a a ciki. Malamai suna fada a wata Ka’ida cewa, “Abin la’akari a mu’amalla shi ne manufa da ma’anonin da suka kunsa, ba wai zahirin lafazi da ginin kalmomi ba”.

"العبرة في العقود بالمقاصد والمعاني، وليست بالألفاظ والمباني"

Amma sabanin masana ko malamai a kan wata mas’ala ba shi ne yake nufin an bawa mutane damar yin zabi-ka-tika ta hanyar mutum ya zaba wani ra’ayi kurum ya darje shikenan ba! Mutum yana zabar maganar da tafi tsayawa a kan dalilan Kur’ani da Sunna ne kurum, ba wai ya bi yarima a sha kida ba! Ko ya bi hanyar tsanantawa mara tushe! Imamu Sufyanu Assauri yana cewa, “Ilimi a wurinmu shi ne samun rangwame daga yardajjen malami. Amma matsantawa kuwa, wannan kowa zai iya yinta”.-(Jami’u Bayanil Ilimi Wa Fadlilihi na Ibnu Abdilbarri: 2/77/ 766)

قال الإمام سفيان الثوري رضي الله عنه أنه قال إنما العلم عندنا الرخصة من ثقة، فأما التشديد فيحسنه كل أحد".

Allah ya bamu tsayawa a kan neman halal da kauracewa haram bisa yadda Shari’a ta tsara. Ya bamu ikon tsayawa a kan tsarin addininmu da bin sahun Annabinmu – Tsira da Amincin Allah su kara tabbata a gareshi da Alayensa da Sahabbansa bakidaya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel