Kwana uku jere: Yan Najeriya sama da 3000 sun kamu da cutar Korona

Kwana uku jere: Yan Najeriya sama da 3000 sun kamu da cutar Korona

- Ko shakka babu yanzu, an shiga babin annobar korona 2.0

- Alkaluman masu kamuwa da kwayar cutar sai kara hawan gwauron zabi suke yi a 'yan kwanakin baya bayan nan

- Gwamnati ta bada umurnin rufe makarantu, gidajen biki, gidajen rawa kuma an dakatad da bukukuwan Kirismeti

Alkaluman baya bayan nan akan mutanen da annobar cutar korona ke kamawa a Nigeria sun nuna cewa ko shakka babu an koma gidan jiya.

Mutane 1041 kwayar cutar ta harba a fadin Nigeria a ranar Alhamis, 24 ga watan Disamba, kamar yadda ya ke a sakon sanar da alkaluman sabbin mutane da cutar ke kamawa wanda NCDC ta saba fitarwa kullum.

Adadin da aka samu ranar Alhamis ya kai jimillan wadanda suka kamu da cutar 81,963 a Najeriya.

Daga cikin sama da mutane 80,000 da suka kamu, an sallami 69,651 yayinda 1242 suka rigamu gidan gaskiya.

Daga ranar Talata zuwa yanzu, sama da mutane 3000 suka kamu a Najeriya.

Kwana uku jere: Yan Najeriya sama da 3000 sun kamu da cutar Korona
Kwana uku jere: Yan Najeriya sama da 3000 sun kamu da cutar Korona Hoto: @NCDCgov
Asali: Twitter

Ga jerin jihohi da adadin da suka kamu:

Lagos-316

FCT-210

Kaduna-83

Plateau-70

Gombe-56

Oyo-56

Katsina-47

Nasarawa-35

Kano-33

Ogun-21

Rivers-17

Niger-14

Imo-14

Delta-12

Kwara-12

Edo-12

Benue-9

Anambra-8

Taraba-4

Ekiti-4

Ebonyi-6

Bayelsa-1

Sokoto-1

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel