Da duminsa: Dalibai sun fito zanga-zanga a jihar Kano kan umurnin rufe makarantu
- Bayan rufe sakandare, za'a rufe jami'o'in jihar Kano daga ranar Laraba
- Kwamishanar ilmin manyan makarantu ta sanar da hakan a jawabi
- Daliban daya daga cikin makarantun Kano sun nuna rashin amincewarsu da haka
Daliban kwalejin Ilimin Sa’adatu Rimi dake jihar Kano sun fito gudanar da zanga-zangan nuna rashin amincewa da umurnin rufe makarantu gaba da sakandare da gwamnatin jihar tayi.
Rahoto daga gidan rediyon Arewa 93.1 na nuna cewa daliban makarantar dake karamar hukumar Kumbotso sun tare hanyar titin Kano zuwa Zaria.
Hakan ya kawo tsaiko ga matafiya dake bin hanyar yanzu haka.
DUBA NAN: Gwamna Matawalle ya kulle makarantun Zamfara dake makwabtaka da Katsina da Kaduna
Mun kawo muku cewa gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ta bada umurnin rufe jami'ar Bayero da sauran makarantun gaba da sakandaren dake jihar ba tare da bata lokaci ba, rahoton Daily Trust.
Wannan sanarwan ya zo kwana daya bayan gwamnatin jihar ta kulle dukkan makarantun firamare da sakandaren dake jihar.
A jawabin da kwamishanar ilmin makarantun gaba da sakandare, Dakta Mariya Bunkure, ta rattafa hannu, an umurci dukkan dalibai su koma gidajensu.
"Muna shawartan dukkan dalibai su fita daga cikin makarantu daga ranar 16/12/2020," tace.
Hakazalika, gwamnan Kano ya bayar da umarnin rufe dukkan makarantun gwamnati da masu zaman kansu da ke fadin Jihar.
Gwamnatin jihar Kano ba ta bayyana dalilin rufe makarantun ba a cikin gajeriyar sanarwar da kwamishinan ilimi, Sanusi Kiru, ya fitar.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng