Amfanin da lemon tsami ya ke da shi ga lafiyar maniyi
- Lemon tsami na dauke da sinadaran Vitamin C da B, wanda ke da kaso 51 na bukatuwar jikin Dan Adam na wannan sinadarin a kowacce rana
- Bincike ya nuna cewa akwai alaka mai karfi tsakanin lemon tsami da maniyin namiji, musamman ta bangaren samar da kwan halitta
- Sai dai fa, duk da tarin amfanin lemon tsami ga lafiyar maniyi, a hannu daya, yana da tarin illoli ga lafiyar mutum, musamman masu cutar olsa
Saboda sinadaren da lemon tsami ya ke dauke da shi, likitoci suka lissafa shi a cikin yayan itatuwa masu matukar muhimmanci ga lafiyar dan Adam.
Duk da cewa, a yankin Afirka da Asiya, nau'in lemon tsami guda daya ne aka fi sani, dan karami mai tsami, sai dai akwai nau'ikan lemon tsamin daban daban a sassan duniya.
Kamar yadda binciken mujallar lafiya ta Healthline ya nuna, lemon tsami na samar da 31mg na sinadarin Vitamin C, kasho 51 na bukatuwar jikin dan Adam na sinadarin a kowacce rana.
KARANTA WANNAN: Dalilai da suke nuna bukatuwar shan lemun tsami a kowace safiya
DUBA WANNAN: Kawar da warin jiki da sirrika 8 na lemun tsami ga lafiyar dan Adam
Haka zalika, lemon tsami na dauke da sinadarin Iron da Calcium, hadi da Vitamin B da Potassium, har ma da sinadarin Magnesium.
Bincike ya nuna cewa akwai alaka mai karfi tsakanin lemon tsami da maniyin namiji, musamman ta bangaren samar da kwan halitta, yana taimakawa wajen kara karfin gudun maniyi.
Alakar lemon tsami da maniyi
Bincike ya nuna cewa akwai alaka mai karfi tsakanin lemon tsami da maniyin namiji, musamman ta bangaren samar da kwan halitta, yana taimakawa wajen kara karfin gudun maniyi.
Akwai sinadaran Vitamin C da thiamine a cikin lemon tsami, wanda ke bunkasa kwan haihuwa ta hanyar kara karfi ga maniyi.
Dangane da ikirarin wasu na cewar lemon tsami na tsinka maniyi, Hajiya Jummai Hassan wacce kwararriyar likita ce kan abinci a asibitin Wuse a Abuja, ta karyata hakan.
KARANTA WANNAN: Illoli 6 na lemun tsami ga lafiyar ɗan Adam
Ta bayyana cewa ruwan lemun tsamin da ake matsawa a ruwa ko a shayi a sha bai kai yawan da zai tsinka maniyi ba, illa ma dai zai gyara da inganta shi.
Sai dai wani bincike da aka gudanar a kasar Australia na nuni da cewa, shan lemon tsami mai yawa a lokaci daya na tsinka maniyi, hakan illa ne ga iyalan da ke son ba da tazarar haihuwa.
Yadda maza za su yi amfani da lemon tsami don bunkasa maniyi
Matakin farko na amfani da lemon tsami shine yin amfani da shi a lokacin da aka yanka shi. Za a iya amfani da shi a ruwa, salads, zuma ko a cikin shayi, wani lemon ko cinnamon.
Ka samu ruwa kofi daya, ka matsa lemun tsami guda daya, idan kana so, ka hada da zuma. Irin wannan hadin ana so a shashi kafin ayi karin kumallo.
Bincike ya nuna cewa cin yayan itatuwa masu dauke da sinadarin Vitamin C kamar lemon tsami, na rage hatsarin kamuwa da cutar zuciya ko shanyewar rabin jiki.
Illolin lemon tsami ga lafiyar maniyi
Masana kiwon lafiya sun tabbatar da cewa, duk da tarin amfanin lemon tsami ga lafiyar dan Adam, hakan bai hana lemon tsamin zama mai illa ba, musamman ga masu ciwon gyambon ciki.
Kasancewar lemon tsami na dauke da sinadarin asid mai yawa, kuma gyambon ciki (ulcer) na gaba da asid, hakan na iya daga ciwon da zaran mai dauke da shi ya sha lemon tsami.
Kwararriyar likitar abinci a asibitrin Wuse Hajiya Jummai, ta bayyana cewa, lemon tsami yana illa ne kawai ga masu dauke da cututtukan da ke adawa da asid a cikinsu.
Ga mutanen da jikinsu ke zabar nau'ikan abincin da suke so, da yawansu lemon tsami na sanya su yin amai ko zafin zuciya da kumburin jiki, a cewar mujallar Healthline.
TSOKACI:
An wallafa wannan rubutun don ilimantarwa kawai, ba ayi shi domin togaciya ka mutum daya ba kawai. Haka zalika, ba zai zama madadin shawarar kwararru ba, don haka kada ayi amfani da shi wajen taimakon kai-da-kai, a nemi taimakon likitoci kawai. Duk wani bayani da ka dauka a rubutun nan kayi amfani da shi, to ka yi ne a kashin kanka, kuma kaine ke da alhakin ko me zai je ya zo.
INDA AKA SAMO BAYANAI:
1. Amfanin lemon tsami (2018 healthline.com)
2. Sinadaren da ke jikin lemon tsami (2019 medicalnewstoday.com)
3. Muhimmancin lemon tsami ga lafiyar maniyi (2020 bbc.com/hausa)
4. Amfanin lemon tsami ga maniyi (2016 sciencedirect.com)
5. Illolin lemon tsami ga maza (2020 emedihealth.com)
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng